Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Kwamitin Zakka Na Jihar Sokoto


Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

Rahotanni daga jihar Sokoto dake arewacin Nijeriya sun ce wasu 'yan bindiga da ba'a tantance ko su wene ne ba, sun sace shugaban kwamitin zakka da wakafi na jihar Sokoto, Mallam Muhammad Lawal Maidoki.

An sace Malam Maidoki ne a kan hanyar sa ta dawowa Sokoto daga Birnin Gwari ta jihar Kaduna, inda ya tafi gaisuwar ta'aziyya.

'Yan bindigar sun yi awon gaba da malamin ne tare da matar sa da matar kaninsa da kuma kanwar sa da suke tafiya tare a mota daya, inda suka sanya su a wata motar, suka kuma umarci direban malamin da ya wuce gida da motarsu.

Duk da yake kawo yanzu ba'a san inda malamin da matan suke ba, to amma wasu majiyoyi sun ce tuni dai 'yan bindigar suka yi magana da iyalan malamin, inda suka nemi a biya kudin fansa domin a sako mutanen. 'Yan bindigar na neman nera miliyan hamsin akan kowane, wato jimillar nera miliyan dari biyu ke nan

'Yan bindigar su gargadi iyalan malamin da kada su kuskura su yi magana da 'yan jarida, ko kuma su kashe su.

Lamarin kuma an kai rahoton sa ne ga rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, don haka 'yan sandan Sokoto sun ce basu da cikakken bayani akan lamarin.

Murtala Faruk Sanyinna.

XS
SM
MD
LG