Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Dalibai Shida Da Malamai Uku A Kudu Maso Yammacin Najeriya


Yan bindiga
Yan bindiga

A ranar Litinin da daddare ne wasu ‘yan bindiga a Najeriya suka yi garkuwa da dalibai shida da malamai uku daga wata makaranta da ke kudu maso yammacin jihar Ekiti, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana a ranar Talata, a wani rahoton na sace yara ‘yan makaranta da aka yi a kasar na farko bana.

WASHINGTON, D. C. - Wasu gungun ‘yan bindiga ne suka yi garkuwa da mutanen kauyuka da matafiya da dalibai domin karbar kudin fansa, yayin da kasar da ta fi kowacce yawan al’umma a Afirka ke fama da matsalar rashin tsaro, wanda kuma ya hada da matsalar ‘yan tada kayar baya na Islama a yankin arewa maso gabas.

Yan bindiga
Yan bindiga

A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar Ekiti ta fitar ta ce an yi garkuwa da daliban ne da malaman a lokacin da suke dawowa daga balaguron gida a daren ranar Litinin. Haka zalika an dauke duk da direban bas din makarantar.

Sanarwar ta kara da cewa, jami'an tsaro a jihar na kan bin sawun wadanda suka yi garkuwa da su.

Babu wanda ya dauki alhakin ko ya nemi kudin fansa.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)

Shugaba Bola Tinubu, wanda ya mayar da hankali wajen farfado da tattalin arzikin kasar da ya tabarbare, na fuskantar karin bincike kan yadda aka yi ta yin garkuwa da mutane a fadin Najeriya, ciki har da a wajen Abuja babban birnin kasar cikin wannan wata.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

Jagoran ‘yan adawa Atiku Abubakar a ranar Talatar ya zargi Tinubu da “yin wasa a lokacin da Najeriya ke nutsewa cikin rashin tsaro,” yana mai nuni da ziyarar da shugaban ya kai kasar Faransa na kashin kansa na tsawon mako guda.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG