Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Najeriya Na Kokawa Game Da Tsarin Fara Biyan Kudin Tikitin Jirgin Saman Fita Waje Da Dala


Tsarin fara sayen tikitin jirgin saman fita waje da kudin dala da aka sanar cewa wasu kamfanonin jiragen sama zasu yi ya fara aiki a ranar 19 ga watan Afrilun nan da muke ciki.

ABUJA, NIGERIA - ‘Yan Najeriya ciki har da dalibai dake karatu a kasashen waje, yan kasuwan canji, da wasu ‘yan kasuwa masu fita wajen sarin kaya sun fara kokawa a kan tasirin hakan ga harkokinsu na yau da kullum.

A ranar 19 ga watan Afrilu ne wasu daga cikin kamfanonin jiragen saman kasashen waje da ke jigilar fasinjoji zuwa Najeriya karkashin yarjejeniyar kungiyar APG Interline suka fara aiwatar da tsarin da suka sanar na sayar da tikitin jirgin sama a kudin dala a daidai lokacin da ake fama da matsalar karancin kudaden wajen a Najeriya.

Wannan matakin da kamfanonin jiragen saman suka dauka dai ya biyo bayan matsalolin da suke fuskanta wajen maido da kudaden tikitin da aka saya a kasar zuwa ga lalitar su wadanda suka makale a Najeriya da wasu kasashe, tare da tabarbarewar kudaden kasashen wajen.

Alkaluman kididdiga sun yi nuni da cewa kudaden sayen tikitin dillalan kasar waje a Najeriya sun kai dala miliyan 283 kwatankwacin Naira biliyan 116 da militant 870 a kwanan nan.

Sanannen dillalai a kan dandamali na APG IET da suka shiga wannan tsarin biyan tikiti da dala sun hada da jirgin saman Afirka ta kudu, Fly Dubai, Kenya Airways, jirgin saman gabas ta tsakiya, Royal Air Maroc, Riwand Air, jirgin saman Thai Air, Turkish Airlines, Bee French Bee, Egypt Air, ASKY, Air Seychelles, Air Algerie, da kuma Air Namibia.

Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulrauf:

Wasu ‘Yan Najeriya Na Kokawa Game Da Tsarin Fara Biyan Kudin Tikitin Jirgin Saman Fita Waje Da Dala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

XS
SM
MD
LG