Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Najeriya Sun Ce Marasa Aikin Yi Ne Ke Neman A Raba Kasar


A daidai lokacin da gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya wato CNG ke nesanta kai da gwamnonin kudu da ayyukan kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafara da neman kasa ta ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya wasan yara ne kawai, wasu na cewa ‘yan Najeriya mara sa aikin yi ke neman a raba kasar.

Gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya dai ta kara jaddada hatsarin da ke tattare da ci gaba da zama da kungiyar IPOB da ke ci gaba da sanya al’umman da basu ji ba su gani ba zaman dar-dar a cewar shugaban kwamitin amintattun Nastura Ashir Sharriff.

CNG ta ce, nesanta kai da gwamnonin kudu suka yi da matasan IPOB wasan yara ne kawai saboda su, suka cusawa matasansu akidar Biafra don ba su da wayo a lokacin yakin basasa tare da cewa kamata ne gwamnati ta bi tsarin raba gardama wato referendum don ba su damar ballewa daga Najeriya don a samu zaman lafiya.

Ra’ayoyin wasu ‘yan kasuwa a binin tarayya Abuja, sun banbanta inda wasu ke cewa, matasa mara aikin yi ke neman a raba kasa saboda suna da kyakkyawar dangantaka da ‘yan kabilar Igbo a wuraren sana’o’insu.

Daga karshe kungiyar CNG ta ce, arewa ba za ta ci gaba da fadawa yaudarar shugabannin kudu ba ta na mai mika bukatar a ba su damar kafa kasar su ta Biafra a bisa tsarin doka daga majalisun kasar.

Da maraicen ranar asabar ne kungiyar gwamnonin kudu maso gabas ta nesanta kan ta da ayyukan kungiyar IPOB tare da nuna goyon bayan ta da Najeriya ta ci gaba da kasancewa a matsayin kasa dunkulalliya.

Idan ana iya tunawa, a shekarar 2012 ne Nnamdi Kanu ya kafa kungiyar IPOB inda gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ta a matsayin haramtaciyya bayan wasu taho-mu-gama da jami’an tsaro a yankunan kudu sakamakon ayyukan kungiyar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulra’uf:

Wasu ‘Yan Najeriya Sun Ce Marasa Aikin Yi Ne Ke Neman A Raba Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi

Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:05 0:00


XS
SM
MD
LG