Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Majalisar Dokokin Adamawa Suna Barazanar Canza Sheka


Jihar Adamawa

Biyo bayan rushe kwamitin shugabannin jam'iyyar PDP na jihar Adamawa wasu 'yan majalisar dokokin jihar suna shirin barin jam'iyyar su shiga APC domin nuna fushinsu.

'Yan majalisar kusan su 23 daga cikin 25 na kokarin barin jam'iyyar idan har uwar jam'iyyar ta tsaya akan rushe shugabannin jihar.

Mr. Solomon Kumanga sakataren kakakin majalisar Ahmadu Fintiri ya tabbatar da yunkurin tare da bayyana dalilan da yasa 'yan majalisar na son daukar matakin.

Shugabannin da aka rusa suna shirin shirya wani gangami domin nuna fushinsu. Chief Joel Madaki tsohon shugaban jam'iyyar da aka rusa yace su fa suna nan daram. Yace an sha basu dan takarar da basa so to amma a wannan lokacin ba zasu yadda ba. Yace zasu je kotu domin ita ce karshe.

Amma wani kusa a jam'iyyar kuma dan takarar gwamna Dr Umar Ardo ya umurci wadanda aka rusa cewa saidai su je kotu. Bisa ga tsarin mulkin PDP kwamitin shugabancin jam'iyyar na kasa nada ikon rusa kowane kwamitin jiha. Amma akwai ka'idodin yin hakan.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

XS
SM
MD
LG