Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Fashewa Ta Hallaka Mutane 19 a Ingila


‘Yan sandan Birtaniya sunce a kalla mutane goma sha tara aka kashe wadansu hamsin kuma suka ji raunuka a wata fashewa da ta auku jiya Litinin a kofar wani dakin wasa a Manchester, Ingila.

Muna daukar lamarin a matsayin ta’addanci har sai mun sami Karin bayanai inji Ian Hopkins, babban jami’in ‘yan sanda na Manchester.

Hopkins yace fashewar ta faru ne bayanda Ariana Grande wata fitacciyar mawakiyar Amurka ta kammala wasan kade, yace ‘yan sandan birnin suna aiki tare da hadin guiwar hukumomin yaki da ta’addanci na kasa.

Grande ta rubuta a shafinta na twitter cewa, “Ina bakin ciki. Daga birnin zuciyata, ina bakin ciki.

PM Birtaniya Theresa May ta jajintawa wadanda harin ya shafa, ta kuma yi allah wadai da harin ta’addancin.

Fashewar ta auku ne a katanfaren dakin wasan Manchester mai kujeru dubu ishirin da daya, wanda shine filin wasan cikin daki mafi girma a Turai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG