Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotun Tarayya ta Hana Shugaban Majalisar Dattawa Gurfana a Kotu


Sanata Bukola Saraki shugaban majalisar dattawa.

Yau Juma'a ake zaton Dr Bukola Saraki shugaban majalisar Dattawan Najeriya zai gurfana gaban kotu ya amsa zargin da ake yi masa amma wani alkalin babban kotun tarayya ya hana.

Ma'aikatar shari'ar kasar Najeriya ta shirya tsaf ta gurfanar da Dr. Bukola Saraki shugaban majalisar dattawa gaban wani kotu yau Juma'a.

Ma'aikatar ta tsara tuhume tuhume har guda goma sha uku akan shi Dr Bukola Saraki da zata gabatar yau. To amma kwatsam sai wata kotun tarayya dake karkashin mai shari'a Ahmed Muhammad ta dakatar da gurfanar da shugaban majalisar gaban kotu har sai ta saurari karar da aka shigar gabanta.

Kotun tarayyar ta gayyato ma'aikatar shari'a da shugaban hukumar da'a ta kasa da shugaban kotun da aka shirya gurfanar dashi Bukola Saraki duka su bayyana a gabanta ranar 21 ga wannan watan domin su bayyana mata dalilan da suka sa za'a gurfanar da Dr. Bukola Saraki gaban kotun.

Kazalika a cikin wadanda aka gayyato sun hada ma da wani mataimakin darakta a ofishin atoni janar na tarayya Mr. Muslim Hassan.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG