Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotun Uganda Ta Ki Amincewa Da Yunkurin Soke Dokar Hana Luwadi Da Ta Tanadi Hukuncin Kisa


Uganda Anti Gay Law
Uganda Anti Gay Law

Kotun tsarin mulkin Uganda a ranar Laraba ta amince da dokar hana luwadi da ta ba da damar yanke hukuncin kisa duk da Allah wadai da kungiyoyin kare hakkin dana dam da sauransu ke yi a kasashen waje.

President Yoweri Museveni signed the bill into law in May last year. The law is supported by many in the East African country, where some see it as behavior imported from abroad and not a sexual orientation.

Shugaba Yoweri Museveni ya sanya hannu kan dokar a watan Mayun bara. Wasu da dama a wannan kasa ta gabashin Afirka na goyon bayan dokar, inda wasu ke ganin luwadi a matsayin dabi’ar da aka shigo da ita daga kasashen waje kuma ba yanayin halitta ne na ainihi ba.

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni.
Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni.

Wani dan fafatuka mai shigar da kara ya sha alwashin daukaka kara zuwa Kotun Koli.

Alkalan kotun tsarin mulkin kasar sun ce majalisar ta tabbatar da dokar ne bisa ka’ida kuma ba ta saba wa kundin tsarin mulkin kasar ba. Dama luwadi laifi ne a Uganda a ƙarƙashin dokar zamanin mulkin mallaka wadda ke ayyana fasikanci da zina a matsayin laifin wanda ya saba ma “yanayin halitta." Hukuncin wannan laifin shi ne daurin rai da rai.

Wani dan Daudu a kasar Uganda
Wani dan Daudu a kasar Uganda

Wanda ake tuhuma da laifin "yunkurin yin luwadi" za a iya daure shi har na tsawon shekaru 14, kuma laifin "yunkurin luwadi" yana da hukuncin shekaru 10.

Sai dai kotun ta ce kada a rika nuna wa ‘yan luwadi wariya yayin da suke neman waraka.

LGTB - Uganda
LGTB - Uganda

Kwamishinan kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana rashin jin dadinsa da hukuncin kotun, ya kuma yi kira ga gwamnatin Uganda da ta soke dokar.

Bankin Duniya ya dakatar da sabbin lamuni ga Uganda, yana mai cewa daukar karin matakan sun zama dole don tabbatar da cewa ayyukan da bankin ke yi sun yi daidai da irin muhalli da kuma zamantakewar da bankin ke amincewa da su.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG