Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"A Tsige Gwamna Ganduje- Inji Gidauniyar Hamisu.


People take part in the Day of the Dead parade along Reforma avenue in Mexico City, Oct. 27, 2019.

Wata kungiya a Kano ta kalubalancin majalisar dokoki ta jihar ta fara shirin tsige gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje saboda abin data kira keta dokokin kasa da suka shafi bada kwangilar ayyukan gwamnati.

Kungiyar mai suna Hamisu Magaji Foundation mai Ofishi a Kanon, ta ce an karya ka’idar kashe kudin gwamnati wajen bada kwangilar gina gada akan mahadar titin zuwa Gidan Zoo dana Zaria Road akan naira biliyan hudu da rabi.

Shugaban kungiyar Malam Hamisu Magaji ya kira a tsige gwamnan jihar soboda kwangilar bata cikin kasafin kudin jihar na bana

Kimanin makonni uku da suka gabata ne gwamnatin jihar Kano ta bada wannan aiki na gina gada, matakin da tace zai kara kawata birnin Kano.

Sai dai kungiyar ta Hamisu Magaji Foundation tayi zargin cewa, baya ga aringizon kudi da aka yiwa kwangilar an kuma keta ka’idojin kasha kudaden gwamnati.

Malam Hamisu y ace aikin baya cikin kasafin kudin shekarar 2018 da majalisar dokokin jihar Kano ta amince da shi. Sun san an ware N150m kawai saboda aikin hanyar. A tashi fahimtar aikin da ake yi yanzu baya kan tsarin mulki, saboda haka haramtace ne. Yace zasu garzaya kotu domin ta dakatar da aikin ba tare da bata lokaci ba

Shi-kuwa shugaban Jam’iyyar PDP dake hamayya a Jihar Kano Sanata Mas’udu El-Jibril Doguwa, yana cewa aiki ne babba, ba da za’a ce yana cikin rukunin kudin da gwamna zai iya bayarwa. Aikin wai zai jawo ambaliyar zuwa ma mutanen dake zaune a Taraun da Zoo Road. Suna zargin gadar zata kawo nakasu da cunkoso. A cewarsa gara a dauki kudin a sasu inda mutane zasu amfana

To amma, Comrade Mohammed Garba, dake zaman kwamishinan yada labaru na jahar Kano na cewa abu na farko da yakamata mutane su gane shi ne ayyuka ne biyu. Na farko shi ne aikin gadar kasa da zai ci kudi sama da Naira biliyan uku. Da ma can akwai N150m dake cikin kasafin kudin bana. Sannan aiki na biyu shi ne wana baya cikin kasafin kudi, amma gwamnati ta gama tsare-tsare domin ta gabatar da kasafin kudi na musamman da zai kunshi ayyukan.

Tuni kamfanin da aka baiwa wannan kwangila ya fara aiki, bayan da gwamnati ta bashi kashi 50% cikin 100% na adadin kudaden kwangilar wato Naira biliyan 4.5 kuma zai kammala aikin cikin watanni goma masu zuwa.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG