Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Makarantar Mata A Afghanistan Ta Yi Kaura Zuwa Rwanda


Wata daliba tana rubutu a allon da ke lale marhabin da mutane a makarantar SOLA da ke Kabul a Afghanistan (Hoto - shafin yanar gizon makarantar)

A ranar Juma’a an ga Basij-Rasikh tana kona takardun da ke dauke da bayanan daliban makarantar gudun kada ‘yan kungiyar Taliban su binciko su daga baya.

Yayin da kasar Afghanistan ta fada hannun ‘yan kungiyar Taliban, wacce ta haramtawa ‘yan mata zuwa neman ilimin zamani, wata makarantar kwana ta mata daya tilo a kasar, ta koma Rwanda a mataki na wucin gadi.

Shabana Basij-Rasikh, daya daga cikin wadanda suka kafa makarantar wacce ake kira School of Leadership Afghanistan (SOLA) a turance, ta fada a wani sako da ta wallafa a shafin sada zumunta a ranar Talata cewa, daliban makarantar mai zaman kanta su 250, da malamai da iyalan daliban sun bar Kabul babban birnin Afghanistan tun a makon da ya gabata.

“SOLA za ta sauya matsuguni, amma mataki ne na wucin gadi,” Basij-Rasikh ta ce a daya daga cikin jerin sakonnin da ta wallafa a Twitter.

“Yadda muka tsara abin shi ne, za mu kwashe zangon karatu daya ne a kasar waje, idan al’amura suka daidaita, muna fatan za mu dawo Afghanistan.

Basij- Rasikh ta kuma rubuta cewa, ta kasar Qatar suka tafi kasar ta Rwanda wacce ke tsakiyar nahiyar Afirka, inda suke fatan gudanar da karatunsu a can.

Ma’aikatar ilimi a Rwanda ce ta fara amsa wani sakon Twitter da Basij-Rasikh ta wallafa, inda ta ce tana lale marhabin da makarantar ta SOLA a Rwanda.

Mayakan Taliban a lokacin da suka datse hanya
Mayakan Taliban a lokacin da suka datse hanya

Rwanda, na daya daga cikin kasashe da dama da Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce ta amince ta karbi bakunci ‘yan Afghanistan da ake kwashewa a mataki na wucin gadi. Sai dai ya zuwa yanzu, ba a san iya adadin ‘yan Afghanistan da Rwandan za ta karba ba.

A ranar Juma’a an ga Basij-Rasikh tana kona takardun da ke dauke da bayanan daliban makarantar gudun kada ‘yan kungiyar Taliban su binciko su daga baya.

Dandazon mutane suna gudu a gefen jirgin saman dakarun Amurka a filin tashin jirage na Kabul a ranar Litinin 16 ga watan Agusta

Dandazon mutane suna gudu a gefen jirgin saman dakarun Amurka a filin tashin jirage na Kabul a ranar Litinin 16 ga watan Agusta
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:20 0:00

A ranar Talata hukumomin makarantar suka fada a shafin Twitter cewa, suna masu cike da takaici kan halin da kasarsu ta shiga.

“A iya zamana a Kabul, na ga abubuwan tsoro, da fushi da kuma jarumta irin ta ‘yan Afghanistan. Idan na kalli fuskokin dalibaina, na kan ga fuskokin miliyoyin ‘yan matan Afghanistan wadanda aka bari a baya.” Basij-Rasikh ta rubuta.

“’Yan matan ba za su iya ficewa ba, kuma ba zai yi wu mutum ya yi biris da su ba. Idan akwai wani abu daya da zan iya neman alfarma daga duniya shi ne, kada ku dauke hankalinku daga Afghanistan. Kada ku bari hankalinku ya yi wani wuri yayin da makonni ke shudewa. Ku kalli wadannan ‘yan mata, hakan zai sa ku kama masu madafun iko da alhakin abin da zai same su.”

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG