Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Takaddama ta Kunno Kai a Jam'iyyar APC a Jihar Adamawa


APC

Canza shekar da Marcus Gundiri yayi daga APC zuwa PDP makon da ya gabata ta bar kura baya.

Yayin da guguwar canza sheka ke neman zaman kayan ado a faggen siyasar Najeriya wata sabuwa ta kunno kai a jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa.

Canza shekar da Marcus Gundiri yayi ta sa wasu 'ya'yan jam'iyyar ACN dake cikin hadakar da ta haifi APC soma mayarda martani inda suka ce abun da tsohon dan takarar gwamna na jam'iyyar wato shi Gundiri ya yi ba da yawusu yayi ba.

A wurin taron manema labarai wanda ya tsaya da Gundirin a zaben 2011 a matsayin mataimakin gwamna Abdulrazak Nandal yace ba da yawunsu Gundiri ya koma PDP ba. Domin haka Gundiri ya daina cewa ya koma PDP tare da su da kuma yawunsu. Yace shi yana APC kuma ya samu wurin zama.

Sakatariyar APC a jihar Ambassador Fati Bello ta musanta zargin cewa shugabannin jam'iyyar na ficewa. Tace batun ballewa ai a PDP aka fi ballewa inda gwamnoni guda biyar suka fice. Kawo yanzu babu gwamnan APC da ya fita ya koma PDP.

Ga rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG