Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Watakila A Cire Dokar Ta Baci A Adamawa - in ji Tambuwal


Yara Mata a tsaye a wajen wata makaranta dake cikin birnin Maiduguri.

Yayin da aka cika watanni biyu da kafa dokar ta baci a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe, kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Aminu Waziri Tambuwal ya kai ziyara jihar Adamawa inda ya bada tabbacin cewa nan ba da jimawa ba, za'a dage dokar ta bacin da aka kafa.

Hon Aminu Waziri Tambuwal ya bayanna cewa yanzu haka ana nazarin rahotannin da jami’an tsaro ke badawa, game da cigaban da ake samu, bayan kafa dokar ta baci.

Kakakin yace: Na tabbatar, kamar yadda na fada da harshen turanci, nan gaba kadan, mai girma shugaban kasa zai duba, ya ga yanayin da wannan abun yake ciki, domin a samu a dahirta, ga mutan Adamawa a yaye musu wannan dokar da aka saka, ina kyautata zaton bada dadewa ba.

Yana kamalla wannan kalami, sai mutane suka fashe da murna da tafi saboda nuna farin cikinsu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG