Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Winnie Mandela Mai Gwagwarmayar Yaki Da Wariyar Launin Fata Ta Rasu


Winnie Madikizela-Mandela
Winnie Madikizela-Mandela

Winnie Mandela da ta kwashe shekaru tana gwagwarmaya da mulkin wariyar fata a kasarta ta Afirka ta Kudu ta bar duniya jiya Litinin tana da shekaru 81

Jiya Litinin, Allah Ya yiwa Winnie Madikizela-Mandela, wacce ta zama shugabar hadakar yaki da wariyar launin fata, yayinda mijinta wanda daga bisani ya zama shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela yake tsare. Ta rasu tana da shekaru 81 a duniya.

An kwantar da Madikizela Mandela a asibiti a karshen mako saboda tana fama da mura, kuma ta sha fama da da cutar suga ko diabetes a tsawon shekaru.

Da yake bada sanarwar rasuwarta a wani taro da manema labarai ministan makamashi na kasar Jeff Radebe yace "Mrs Mandela tana daya daga cikin jaruman yaki da gwamnatin wariyar launin fata,". Ya kara da cewa ta komawa mahaliccinta tana kewaye da dangi. Radebe ya ci gaba da cewa, ta gwabza gagarumar yaki da tsarin wariyar launin fata, kuma ta sadakar da rayuwarta kaf domin 'yancin kasarta."

Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudun, a jawabinsa ga al'ummar kasar ta talabijin ya ce "Yau mun rasa uwa, mun rasa kaka,mun rasa kawa,mun rasa abokiyar yaki, mun rasa shugaba abar misali ko koyi."

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG