Wani sabon rahoto daga Bankin Duniya na nuni da cewa mutane miliyan 74 ne ke zama cikin talauci a Arewacin Najeriya, wato kowanne mutum hudu daga cikin goma suna rayuwa kullum a kan kasa da dala biyu.
Rahoton ya kuma nuna cewa a shekaru masu zuwa, za a sake samun karuwa ne na wadanda suke cikin talauci.
Rahoton ya kuma nuna cewa yawancin masu talaucin na da zama a Arewacin Najeriya inda wasu dalilai na rayuwa ya sa su cikin talauci tare da zayyana wasu dalilai da suka kawo karin talauci a wannan yanki, kamar rashin aiki, ayyuka marasa tsoka da kuma ayyuka marasa kyau.
Amma rahoton ya kara bayanin yadda tashin hankali na 'yan Boko Haram, da 'yan bindiga wanda ya mayar tada zaune tsaye, na daga cikin muhimman dalilan da suka kara talauci a wannan yanki.
Daga karshe rahoton ya nuna cewa akwai matukar bukatar a shirya wani tsari na mussamman da zai taimakawa matalauta.
Facebook Forum