Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Zamo Wajibi Gwamnati Ta Samar Da Ruwan Sha Mai Tsabta


Mai fama da cutar kwalara a kasar Haiti
Mai fama da cutar kwalara a kasar Haiti

A bayan mummunar annobar kwalara da ta kashe mutane fiye da dubu a Najeriya, an bukaci gwamnati da ta samar da ruwan sha mai tsabta tare da hanyoyin tsabtace muhalli

An bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya da ma na jihohi da su tabbatar da samar da ruwan sha mai tsabta tare da hanyoyin kawar da kazanta da tsabtace muhalli ga al'ummarsu domin kaucewa abkuwar annoba irin ta cutar kwalara da ta ratsa kasar kwanakin baya.

Jami'ar sadarwa ta kamfanin WaterAid Nigeria, Onyinyechi Okechukwu, ita ce ta yi wannan kiran a bayan da annobar cutar kwalara ta yadu ta kashe mutane fiye da dubu daya da dari biyar a kasar a sanadin ambaliyar ruwan da ta baza wannan cuta.

An bayyana wannan annobar kwalara a zaman mafi muni da Najeriya ta gani cikin shekaru 20.

Kamfanin WaterAid yana aiki ne na samar da hanyoyin tsabtace ruwa da kawar da najasa wadanda talaka zai iya morewa, kuma a kwanakin baya kamfanin ya kaddamar da wani kyamfe na wayar da kan jama'a.

Jami'iar ta sadarwar kamfanin WaterAid Nigeria Ms. Okechukwu, ta ce, "Ranar Wanke Hannu ta Duniya da aka gudanar kwanakin baya ta taimaka sosai wajen jaddada muhimmancin wanke hannu da sabulu ko toka a zaman wata hanya mai sauki da arha ta kare kai daga kamuwa da cuta."

Ta ci gaba da cewa, "Kwalara ba ta yin barazana mai muni a kasashen da suka ci gaba irinsu Britaniya da Amurka, kuma ta hanyar tabbatar da hakkin jama'a na sama musu ruwa da hanyoyin tsabtace muhalli, zamu iya mayar da irin wannan annoba ta zamo abin tarihi."

Cutar kwalara tana iya yaduwa kafin kiftawa da Bismillah a duk wani wurin da babu ruwan sha mai kyau ko kuma ake yin najasa a fili, abinda ruwan sama kan wanke ya shigar da shi cikin ruwan shan jama'a.

Kwalara tana kama yara da manya, inda ta ke haddasa zawo mai tsanani tare da hana jikin wanda ya kamu rike ruwa. Wannan yana sa ruwa ya kare a jikin wanda ya kamu, kuma idan har ba a samu an yi maganinta da wuri ba, tana iya kashe mutum cikin 'yan sa'o'i kadan.

A kowace shekara, mutane dubu 120 suke mutuwa daga cutar kwalara. Sai dai kuma, ba lallai ne mutane masu yawan haka su mutu ba domin ana iya rigakafin wannan cuta kuma ana iya warkar da ita cikin sauki.

Kamar sauran cututtukan da ruwa ke yadawa, muhimmin matakin yin rigakafi shi ne tabbatar da tsabtar ruwa, tare da tabbatar da cewa babu ta yadda ruwan sama zai wanke bahaya ya sake shigar da shi cikin ruwan sha. Wanke hannu da yin bahaya cikin shadda su na da matukar muhimmanci.

XS
SM
MD
LG