Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matashi Dan Shekara 23 Ya Yi Wuf Da Amaryarsa 'Yar Shekara 45 A Adamawa

Matashi Dan Shekara 23 Ya Yi Wuf Da Amaryarsa 'Yar Shekara 45 A Jihar Adamawa.
Matashi Dan Shekara 23 Ya Yi Wuf Da Amaryarsa 'Yar Shekara 45 A Jihar Adamawa.

Wani matashi mai shekaru 23 da haihuwa, ya yi wuf da wata sananniyar ‘yar siyasa mai shekaru 45 a jihar Adamawa.

A ‘yan kwanan nan ne labari da hotunan auren wani matashi dan shekaru 23 da ya angwance da amaryarsa mai shekaru 45 ya karade shafukan sada zumunta na yanar gizo.

Matashi Dan Shekara 23 Ya Yi Wuf Da Amaryarsa 'Yar Shekara 45 A Adamawa
Matashi Dan Shekara 23 Ya Yi Wuf Da Amaryarsa 'Yar Shekara 45 A Adamawa

Duk da yake dai rahotannin ba su yi cikakken bayani akan matashin mai suna Adam Dalla ba, to amma kuma an bayyana amaryar ta sa mai suna Barista Jamila Babuba a zaman sananniyar ‘yar siyasa, kuma ‘yar fafutukar a jihar ta Adamawa.

Karin bayani akan: jihar Adamawa, Nigeria, da Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa Honarabul Jamila Babuba, kamar yadda wasu suka fi sanin ta, ta taba yunkurin tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya ta Yola ta Kudu da ta Arewa da Girei a jihar Adamawa.

An wallafa kyawawan hotunan ma’auratan a shafukan twitter da Instagram, hade kuma da katunan bikin auren nasu.

Matashi Dan Shekara 23 Ya Yi Wuf Da Amaryarsa 'Yar Shekara 45 A Adamawa
Matashi Dan Shekara 23 Ya Yi Wuf Da Amaryarsa 'Yar Shekara 45 A Adamawa

An daura auren nasu ne a ranar 18 ga watan nan na Mayu, a yayin da kuma za’a yi bikin auren a ranar 31 ga watan.

Wannan lamari dai ya ja hankalin jama’a da dama, akasari suna jinjina musu, tare da yi musu fatan alkhairi.

Matashi Dan Shekara 23 Ya Yi Wuf Da Amaryarsa 'Yar Shekara 45 A Adamawa
Matashi Dan Shekara 23 Ya Yi Wuf Da Amaryarsa 'Yar Shekara 45 A Adamawa

Haka kuma auren na Dalla da Jamila, ya kara jaddada sabuwar kalmar Hausa ta ‘WUF’ da ake amfani ita domin bayyana irin wannan al’amari.

Wasu da suka yi sharhi kan auren a shafukan sada zumunta, sun bayyana cewa ba yawan shekaru ne abin la’akari ba a yayin neman aure, muddin akwai soyayya da fahimtar juna.

Wasu da dama kuma sun karkata sharhin na su ne ta fuskar addinin ma’auratan wato Musulunci, inda suke bayyana cewa auren na su ma yana da babban tarihi, kasancewar Annabi Muhammad S.A.W ma ya auri matarsa ta farko mai suna Khadija, alhali ta zarta shi a shekaru.

A halin da ake ciki kuma, ana ci gaba da wallafa dubban sharhi akan hotunan auren, a yayin da kuma rahotannin suka bayyana cewa murna ce ta karade a Yola ta jihar Adamawa sakamakon wannan bikin auren.

XS
SM
MD
LG