Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Birnin Dakar Ya Barke Da Murna Bayan Nasarar Senegal A AFCON


'Yan Senegal suna murna a birnin Dakar
'Yan Senegal suna murna a birnin Dakar

Jama’a da dama sun yi ta rera wakoki suna yawo a birnin don nuna farin cikinsu dangane da wannan nasara da ‘yan wasan kasar suka samu.

Jama’a a sassan Dakar, babban birnin kasar Senegal sun fantsama kan titunan birnin don nuna farin cikinsu bayan da ‘yan wasan kasar suka lashe kofin gasar AFCON.

Senegal ta lashe kofin ne bayan da ta doke Egypt da ci 4-2 a bugun feneriti.

Wannan shi ne karon farko da kasar ta lashe wannan kofi.

A shekarar 2019, Senegal ta kai wasan karshe amma ‘yan wasan Aljeriya suka lashe kofin a gasar ta AFCON wacce aka yi a Egypt.

Jama’a da dama sun yi ta rera wakoki suna yawo a birnin don nuna farin cikinsu dangane da wannan nasara da ‘yan wasan kasar suka samu

Wasu sun yi ta zagaya birnin ne a kafa wasu kuma a ababen haha.

Masu murna a birnin Dakar
Masu murna a birnin Dakar

Dan wasan Liverpool Sadio Mane ne ya doka kwallon karshe da ta ba Senegal nasara a gefen ragar Egypt, lamarin da ya jefa tawagar Mohamed Salah cikin yanayi na jimamin shan kaye a wannan wasa.

An ga Mane yana rarrashin abokin wasansa a Liverpool Salah, a lokacin da yake hawaye kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Ita dai Egypt sau bakwai tana lashe kofin gasar, da ta yi nasara a wannan karon, da ya zama karo na takwas kenan da take daga kofin.

Wasan ya kai ga bugun feneriti ne bayan da kasashen biyu suka gaza cin kwallo cikin mintina 120 da aka kwashe ana gwabzawa.

XS
SM
MD
LG