Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan wasan Senegal Sun Isa Kamaru Don Karawa a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka


Lokacin da 'yan wasan Senegal suke sauka a Kamaru (Facebook/Senegal Football Federation)

Senegal ita ce ta zo ta biyu a wasan karshe da ta buga da Aljeriya a gasar ta AFCON ta shekarar 2019. Aljeriya ta doke Senegal da ci 1- 0 ta lashe kofin.

Tawagar ‘yan wasan kasar Senegal “The Lions of Teranga” sun isa Kamaru don shirin fara karawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON.

A ranar 9 ga watan Janairu za a fara gasar. Senegal za ta fara karawa ne da kasar Zimbabwe a ranar Litinin.

Dan wasan Liverpool Sadio Mane da mai tsaron ragar Chelsea Edouard Mendy na daga cikin taurarin ‘yan wasa a tawagar ta Senegal.

“The Lions of Senegal sun isa Kamaru.” Hukumar kwallon kafar kasar ta Senegal ta wallafa a shafinta na Facebook.

'Yan wasan Senegal suna atisaye (Facbook/Senegal Football Nationale)
'Yan wasan Senegal suna atisaye (Facbook/Senegal Football Nationale)

Gabanin kungiyar ta taso daga Dakar, babban birnin na Senegal, an dan samu jinkiri bayan da aka gano wasu 'yan wasa uku da wasu 'yan tawagar tafiyar sun kamu da cutar COVID-19.

Hukumar kwallon kafa ta Senegal ta bayyana sunayen ‘yan wasan a ranar Laraba a matsayin Pape Sarr, Nampalys Mendy da kuma Mame Thiam.

Senegal ita ce ta zo ta biyu a wasan karshe da ta buga da Aljeriya a gasar ta AFCON ta shekarar 2019. Aljeriya ta doke Senegal da ci 1- 0 ta lashe kofin.

Dubi ra’ayoyi

AFCON 2021, Troost-Ekong

Abin da kyaftin Troost-Ekong ya ce da Najeriya ta lashe wasanninta uku a jere bayan doke Guinea-Bissau
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG