Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Buhari, Osinbajo, Gwamnoni Ke Shan Suka Saboda Kin Halartar Jana'izar Attahiru


Shugaba Buhari da mataimakin Osinbajo, a lokacin da suke yi wa marigayi Attahiru kwalliyar karin girma (Twitter/ @BahsirAhmaad)

An yi jana’izarsu a ranar Asabar 22 ga watan Mayu, a makabartar dakarun kasar da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Yan Najeriya musamman a kafafen sada zamunta sun yi ca akan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, saboda kin halartar jana’izar babban hafsan sojin kasar da wasu sojoji da suka mutu a hatsarin jirgin sama.

Laftanar Janar Attahiru ya rasu a ranar Juma’a 21 ga watan Mayu, tare da wasu sojoji 10 yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Abuja.

Jirgin ya fadi ne a kusa da filin tashin jirage na kasa da kasa da ke Kaduna.

An yi jana’izarsu a ranar Asabar 22 ga watan Mayu, a makabartar dakarun kasar da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Sai dai rashin halartar shugabannin biyu, ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan Najeriya, inda jama’a da dama suka raja’a akan cewa kin halartar jana’izar bai dace ba.

Jami'an gwamnatin da suka halarci wajen jana'izar (Twitter/Nigerian Army)
Jami'an gwamnatin da suka halarci wajen jana'izar (Twitter/Nigerian Army)

Ce-ce-ku-cen dai an fi yan shi ne a shafin Twitter.

‘Yan Najeriya da dama sun yi nuni da cewa, jana’izar an yi ta ne a Abuja, saboda haka kamata ya yi a ce sun samu halarta.

Sukar da ake yi, ta shafa har da wasu gwamnoni, wadanda rahotanni suka ce sun zabi harlatar daurin auren wani babban jami'in gwamnati a madadin jana'izar.

Sai dai a lokaci guda, akwai wadanda suka rika nuna rashin halartan shugaba Buhari jana'izar, ba wani abu ba ne, lura da cewa ya tura Ministan tsaronsa.

Kadan daga cikin abin da Sani Lukman ke fada anan shi ne, "akwai sakaci a wannan al'amari, wannan zai iya aikawa jami'an tsaronmu wani bahagon sako," na cewa ba a damu da su ba.

First Daughter cewa ta yi, "Buhari ya tafi har Faransa don halartar wani taro da aka ce "an soke" amma ya kasa tafiya kilomita 15 don halartar jana'izar babban hafsan sojojinsa."

Sai dai Dangaladima kare shugabannin ya yi, inda ya ce "saboda dalilai na tsaro ne" ya sa ba su halarci jana'izar ba bayan da @Nazakk ya ce, "abin kunya ne rashin zuwan Buhari wajen jana'izar."

A wannan muhawara, @golbal_honey ne yake tambayar daya daga cikin hadiman shugaba Buhari Bashir Ahmad "me ya sa mai gidanka bai je jana'izar ba?

Sai dai nan take, @Mr_Othmann ya mayar masa da martani, inda ya ce "dole ne sai ya je?

Hatsarin jirgin saman sojin na zuwa ne sa'o'i bayan dawowar Buhari daga Faransa, inda ya halarci wani taron koli kan tattalin arzikin kasashen Afirka wanda shugaba Emmanuel Macron ya shirya.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, fadar gwamnatin Najeriyar ba ta ce uffan ba, kan dalilin da ya sa shugaba Buhari da mataimakin nasa, ba su halarci jana'izar ba, yayin duk wani kokarin jin ta baki masu magana da yawun gwamnatin ya ci tura.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG