Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Daya Daga Cikin ‘Yan matan Chibok Ta Bayyana Bayan Shekara Bakwai


Ruth Ngladar Pogu, ta biyu daga dama a lokacin da aka gabatar da ita ga gwamna Zulum.(Facebook/Gwamna Zulum)
Ruth Ngladar Pogu, ta biyu daga dama a lokacin da aka gabatar da ita ga gwamna Zulum.(Facebook/Gwamna Zulum)

A ranar 28 ga watan Yuli, Ruth da wani mutum da ta aura, suka mika kansu ga dakarun Najeriya a wani yanki da ke Bama, a cewar wata sanarwa da kakakin gwamna Zulum Malam Isa Gusau ya fitar a karshen mako.

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce gano daya daga cikin daliban makarantar Chibok da aka yi, ya karawa gwamnatinsa kwarin giwar cewa za a kubutar da sauran daliban kuma cikin koshin lafiya.

A ranar Asabar aka gabatar da Ruth Ngladar Pogu ga gwamna Zulum, wacce na daya daga cikin ‘yan mata sama da 200 da kungiyar Boko Haram ta sace shekara bakwai da suka gabata.

A ranar 28 ga watan Yuli, Ruth da wani mutum da ta aura, suka mika kansu ga dakarun Najeriya a wani yanki da ke Bama, a cewar wata sanarwa da kakakin gwamna Zulum Malam Isa Gusau ya fitar a karshen mako.

A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014, mayakan Boko Haram suka far wa makarantar sakandare ta Chibok, suka kwashe dalibai sama da 200 a makarantar.

Wasu daga cikin daliban sun tsere yayin da aka yi nasarar karbo wasu daga cikinsu, amma har yanzu akwai da dama da ba a gan su ba.

“Samun Ruth ya kara kwarin gwiwa ga iyaye, iyalai da gwamnatin jihar Borno cewa za a kubutar da dukkan sauran daliban da ke tsare kuma cikin koshin lafiya.” Sanarwa ta Gusau ta ce.

Sanarwar ta kara da cewa, bayan da aka samu Ruth, gwamna Zulum da jami’an tsaro da sauran jami’an gwamnati sun yi shiru da maganar inda aka kwashe kwana 10 ana tuntubar iyayenta da kuma kungiyar iyayen daliban da suka bata don a tabbatar da asalinta.

“Za a shigar da Ruth wani shiri na musamman don kula da lafiyarta da kuma ba ta dama ta zabi abin da take son ta yi a nan gaba.”

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG