Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako Daliban Makarantar Jangebe


Daliban makarantar Jangebe a lokacin da suka isa fadar gwamnatin jihar Zamfara (Hoto: Twitter, shafin gwamna Matawalle)

Rahotanni daga Najeriya na cewa an sako daliban matan sakandaren Jangebe 279 da aka sace su a jihar Zamfara a makon da ya gabata.

Gwamna Bello Matawalle ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

“Alhamdulillah! Ina mai farin cikin sanar da ku cewa an sako ‘yan matan sakandare na GGSS Jangebe.” Matawalle ya ce.

Daliban Jangebe
Daliban Jangebe

Ya kuma kara da cewa, “hakan ya biyo bayan kalubale da muka yi ta fuskanta wajen kokarin kubutar da su. Ina kira ga ‘yan Najeriya da su taya mu murna domin ‘yan matan sun kubuta.”

Sako daliban na zuwa ne kwana uku bayan da ‘yan bindiga suka kutsa makarantarsu ta kwana da ke Jangebe a karamar hukumar Talata Mafara suka kwashe daliban su 279.

A da rahotannin na nuni da cewa ‘yan matan su 317 ne, amma gwamnatin jihar ta Zamfara ta ce su 279 ne.

A ranar Lahadi an yi ta yamadidin cewa an saki daliban, amma kuma daga baya gwamnatin jihar ta ce ba haka lamarin yake ba.

Wani abu da hukumominm jihar ba su bayyana ba shi ne ko an biya kudin fansa kafin sakin wadannan dalibai.

Sace ‘yan matan ya ja hankalin jama’a a ciki da wajen Najeriya, inda har Asusun da ke tallafa yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi Allah wadai da lamarin ya kuma yi kira ga hukumomin kasar da su yi iya bakin kokarinsu wajen kubutar da su.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Yankin arewa maso yammacin Najeriya musamman jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto da kuma Neja da ke tsakjiyar arewacin kasar, na fama da hare-haren ‘yan bindiga wadanda kan kai hari su kuma sace mutane domin neman kudin fansa.

A baya jihohin Katsina da Zamfara sun yi yunkurin sasantawa da maharan a lokuta da dama, amma lamarin ya cutura duk da zama da aka a matakai daban-daban da ‘yan bindigar.

Wani abu da ba a saba gani ba shi ne yadda shehin malami Sheikh Ahmad Gumi ya dauki ragamar zuwa cikin dazuka domin yin wa’azi ga maharan wadanda akasarinsu Fulani ne.

Sheik Ahmed Gumi Tare da Fulani 'yan Bindiga
Sheik Ahmed Gumi Tare da Fulani 'yan Bindiga

Wannan yunkuri ya janyo mai yabo da kuma suka daga wasu masu sharhi kan al’amuran yau da kullum musamman lokacin da kafafen yada labarai suka ruwaito yadda malamin yake bayyana irin rayuwa ta wahala da al’umar Fulani ke fuskanta a cikin daji.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi watsi da tayin da wasu ke yi na cewa a nemi sasantawa da maharan, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta amince.

Ya kuma yi gargadi ga maharan da su shiga taitayinsu yana mai nanata musu cewa ba wai sun fi karfin hukuma ba ne.

Sace ‘yan matan na Jangebe shi ne karo na biyar da ake garkuwa da dalibai a makarantu daban-daban a Najeriya.

Wasu daga cikin 'Yan Matan Chibok
Wasu daga cikin 'Yan Matan Chibok

A shekarar 2014, mayakan Boko Haram sun sace daruruwan mata dalibai su kusan 300 a garin Chibok da ke jihar Borno, wdanda har yanzu ba a ga wasu daga cikinsu ba.

Lamarin kuma ya janyo kakkausar suka a sassan duniya, ya kuma haifa da ginshikin fafatukar #BringBackOurGirls na neman a sako 'yan matan.

Sai kuma a shekarar 2018, da sake sace wasu jerin dalibai mata su 110 a garin Dapchi da ke jihar Yobe, an saki dukkansu, ban da Leah Sharibu, wacce har yanzu ba a jin duriyarta ba.

Leah Sharibu
Leah Sharibu

A watan Disambar bara an sace wasu dalibai maza sama da 300 a makarantar Kankara da ke jihar Katsina, wadanda su ma tuni an sako su.

Sai kuma a baya-bayan nan da aka sace dalibai 27 da malamansu a makarantar Kagara da ke jihar Neja, wadanda aka karbo su a makon da ya gabata.

Karin bayani akan: Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG