Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Dillalan Man Fetur Ke Korafi Ga Rashin Biyansu Kudin Dakon Mai


Motar Tankar Man Fetur
Motar Tankar Man Fetur

Dilalan man fetur a Najeriya sun yi barazanar daukar kowane irin mataki na ‘yanto kansu daga tanarkin da suka ce gwamnati ta saka su wanda kan yi illa ga sana'ar su.

Kanfanin man fetur na Najeriya ya jima ya na shaidawa ‘yan kasar cewa, ya yi tanadin isashen mai da zai wadaci bukatun kasar na tsawon lokaci, sai dai dakon man ne ke fuskantar kalubale abinda ya sa ake ta samun dogayen layuka da kuma tsadar man a wasu sassan kasar.

Su kuwa dilalan mai ‘yan kasuwa sun jima suna kokawa akan cewa gwamnati bata biyan su, kudin dakon man yadda ya kamata abinda ya sa suke biyar biliyoyin nairori.

To har yanzu dai zancen bai sauya ba, domin yanzu haka ma suna kan tattaunawa don daukar kowane mataki na ganin sun samu fita daga yanayin barazana da suka ce suna fuskanta.

Sirajo Yahaya Kamba shugaban kungiyar dilalan mai na depot na Gusau yace wata goma sha daya ba'a biya su kudin dakon ba.

To sai dai dama wasu jama'a a ganin suma dilalan ba zasu rasa nasu laifi ba, abinda kuma daya daga cikin su ya shaida cewa suma fa suna da gudunmuwar zasu bayar ga samarwa talaka sauki.

Akasarin lokutan da aka samu wata tankiya tsakanin hukuma da kungiyoyin kwadago ko na ‘yan kasuwa daga karshe talaka shine ke shan ukuba, kuma ba zai iya hana faruwar hakan ba, abinda ya sa wasu ke ganin yana da kyau kowa ya yi adalci a hakkin da ya rataya a kansa.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
XS
SM
MD
LG