Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Mutuwar Hanifa Za Ta Iya Kawo Canji a Cin Zarafin Kananan Yara: Halima Shekarau


Yadda Mutuwar Hanifa Za Ta Iya Kawo Canji a Cin Zarafin Kananan Yara
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:52 0:00

Yadda Mutuwar Hanifa Za Ta Iya Kawo Canji a Cin Zarafin Kananan Yara

Mai dakin tsohon gwamnan jihar Kano Hajiya Halima Ibrahim Shekarau, ta ce ya kamata garkuwa da kuma kashe Hanifa Abubakar da aka yi, ya sa hukumomi da daidaikun jama’a su sake lale a daukar matakin kare kananan yara,

A hirar ta da Muryar Amurka yayin ziyarar jaje da ta kaiwa iyayen Hanifa Abubakar, ‘yar shekaru biyar da ake zargin Abudulmalik Tanko ya yi garkuwa da ita, daga nan ya kashe ta, ta ce, kamata ya yi a rika gaggawar tuhuma da kuma hukumta dukan wadanda ake kamawa da irin wannan laifin.

Bisa ga cewarta, tara irin wadannan mutanen a gidajen yari ba alheri ba ne ga al’umma, domin jama’a za su ga ba a komi. A maimakon haka, za a ci gaba da samun masu aikata irin wadannan laifuka kasancewa ba a dauki matakin da zai iya zama ishara ga wadansu ba.

Hajiya Halima ta bayyana takaicin ganin yadda ake kama masu yiwa kananan yara fyade ko kuma cin zarafin kananan yara da aka sani suna zaune tsakanin al’umma, da wadansu lokuta akan kama su a kaisu ofishin ‘yan sanda. ‘Yan sanda kuma sun san da zamansu, kuma sun amsa laifukan, amma a karshe ba a sake jin abinda ya biyo baya.

Ta yi misali da yadda wani tsoho ya fada da bakinshi cewa, ya yi wa wata karamar yarinya ‘yar shekaru uku fyade. Tace jin iri-irin wadannan labaran a matsayin uwa tilas ne hankali ya tashi.

Lokacin da Gwamna Ganduje ya je ta'aziyya gidan iyayen Hanifa
Lokacin da Gwamna Ganduje ya je ta'aziyya gidan iyayen Hanifa

Mai dakin tsohon gwamnan jihar Kanon tace, ya kamata abinda ya faru da Hanifa ya sa hukumomi su farga, su dauki matakin a kan masu garkuwa da mutane da kuma yi wa kananan yara fyade ko cin zarafin su ta kowacce fuska. Tace tilas ne hukumomi su rika tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Bisa ga cewarta, daukar matakin gaggawa kuma tsats-tsaura zai sa duk mai tunanin aikata irin wannan laifin sake tunani.

Hajiya Halima tace, a matsayinsu na iyaye, ba zasu lamunci ci gaba da cin zarafi da kuma kashe kananan yara ba sabili da sakacin al’umma. Ta ce ba ta san Hanifa ko kuma iyayenta ba, amma duk mace ta san dadin da, ta kuma san zafin rasa shi. Sabili da haka, take kira ga hukumomi su dauki matakin kare rayukan kananan yara.

Hanifa Abdullahi
Hanifa Abdullahi

Hanifa Abubakar ‘yar shekaru biyar da haihuwa, kuma ‘ya daya tilo ga mahaifanta Abubakar Abdulsalam da Murja Suleiman, ta rasa ranta ne bayan da aka yi zargin cewa, mai makarantar da ake kira Nobel Kids dake Kwanar Dakata, Karamar Hukumar Nassarawa, jihar Kano, ya yi garkuwa da ita, daga nan ya kashe ta da maganin bera.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG