Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Wata Mata Ta Kashe Kishiyarta A Minna


Babban Kotun Tarayya a Legas.

Rundunar 'yan sandan jihar Neja Najeriya ta ce tana bincike akan wata mata 'yar kimanin Shekara 24 mai suna Amina Aliyu bisa zargin yi wa kishiyarta kisan gilla a unguwar Tunga da ke cikin fadar gwamnatin jihar ta Neja.

Hukumomi dai sun ce Amina Aliyu tana hannunsu, kuma tana amsa tambayoyi kan kisan kishiyarta mai suna Fatima Ibrahim yar kimanin shekaru 17. ta hanyar rabka mata itace da kuma yunkurin konata ta hanyar banka ma dakinta wuta.

A hirar shi da Muryar Amurka, Alhaji Aliyu Abdullahi, mijin matan guda 2 wadda aka kashen dake zaman Amarya da Uwar gida da ake zargin ta yi kisan yace yana cikin wani yanayi na tashin hankali.

Karin bayani akan: Amina Aliyu, Minna, Fatima, Nigeria, da Najeriya.

Alhaji Abdullahi ya bayyana cewa, bai taba tunanin wannan lamarin zai iya faruwa a gaidansa ba. Bisa ga cewarshi, uwargidansa ta kashe kishiyartan ne tare da taimakon kanwarta wadda suka hadu suka buge ta da tabarya kuma bayan ta mutu su ka yi kokarin cinnawa dakinta wuta. Ya kuma yi kira ga hukumomi da jami’an ‘yan sanda su ci gaba da gudanar da bincike a kan wannan lamarin.

A na shi bayanin, Malam Ibrahim Yahaya Sidi, mahaifin marigayiya Fatima yace yana fatan hukumomin za su bi masa hakkin diyarsa da aka kashe.

Gwamnatin jihar Nejan dai tace tasamu wannan Labari kuma za ta yi duk abinda ya wajaba domin tabbatar da an hukunta mai laifi inji daraktar kula da ma'aikatar kare hakkin mata da yara a jihar Barista Maryam Kolo. Ta ce hukumomi za su tabbatar an gudanar da cikakken bincike an kuma yanke hukumci yadda ya kamata.

Shi ma a nasa bayanin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Nejan Adamu Usman yace a yanzu suna rike da Mutane 4 akan wannan al’amari .

Tuni dai aka kai gawar Fatima gidan mahaifinta dake jihar Katsina kuma aka gudanar da jana’izarta da yammacin Laraban nan.

Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari cikin sauti:

Wata Mace Ta Kashe Kishiyarta A Minna-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG