Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki da Kungiyar ISIS Zai Dauki Lokaci - Obama


Shugaba Barack Obama.

Shekara daya bayan da Amurka ta jagoranci kawanceen wasu kasashe saboda yaki da kungiyar ISIS, shugaba Obama ya bada rahoto a taron da ya shugabanta aMajalisar Dinkin Duniya

Shekara daya bayan yekuwar da ya yiwa shugabanin duniya su fito da shiri na musamman na samun galaba kan kungiyar ISIL ko ISIS, shugaban Amurka Barack Obama, jiya Talata a Majalisar Dinkin Duniya, ya gabatar da rahotonci gaba da aka samu, tareda sako cewa yaki da masu irin wannan tunani ba zai kasance da sauki ko a gama shi cikin wani dan gajeren lokaci ba.

Da ya jagoranci wani taron koli kan hanyoyin shawo kan kungyar ISIL da masu zazzafar ra'ayin addini, a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya, Mr. Obama yace fiye da kasashen duniya 100, da hukumomi ne suka amsa kiran da yayi na hada karfi tsakanin hukumomin duniya da zummar ganin bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi.

Shugaban na Amurka yace kasashe da suka hada da Najeriya da Tunisia da Malaysia sun shiga sahun kasashe sama da 60 wadanda Amurka take yiwa jagoranci a fafatawa da ake yi da kungiyar ISIL a Iraqi da Syria, a lamari da ya kira gwagwarmaya da zata sami nasarori da kuma koma baya a wasu lokuta.

Mr. Obama yace Kungiyar ISIS ta yi karfi a wasu sassan Iraqi da Syria a wuraren da babu tsaro, kuma ya yarda kungiyar ta gawurta wajen amfani da dandalin sada zumunci wajen jayo hankalin matasa su shiga kungiyar.

Shugaba Obama a jiya Talatan ma, ya sake nanata abunda ya kira , bukatar gano musabbin bullar kungiyar ISIS da sauran kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayin addini.

Shugaba Obama yayi kira ga shugabannin kasashen duniya su tunkari matsalolin siyasa da tattalin arziki da masu tsatsauran ra'ayi suke amfani dasu wajen jawo hankali mutane su goyi bayansu.

XS
SM
MD
LG