Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Afirka Miliyan 75 Suka Bada Cin Hanci Bara - Transparency International


Preap Kol babban darakta na Transparency International
Preap Kol babban darakta na Transparency International

Kungiyar Transparency International da ke yaki da matsalar cin hanci da rashawa, ta yi kiyasin cewa, akalla ‘yan kasashen Afrika miliyan 75 ne suka ba da cin hanci a shekarar da ta gabata.

Wani rahoto da kungiyar ta fitar, ya nuna cewa, mafi yawan ‘yan Afrika, sun yi amannar cewa matsalar ta hanci, na ci gaba da karuwa a nahiyar.

Masu gudanar da binciken sun yi nazari ne akan mutane dubu 43 da suka fito daga kasashen da ke Kudu da Hamada, wadanda aka tambayesu ra’ayinsu da kuma yadda suke kallon matsalar ta cin hanci da rashawa.

Kashi 58 daga cikinsu, sun ce matsalar ta karu a watannin goma-sha-biyun da suka gabata.

Mafi yawan shugabannin Afrika, sun kan sha alwashin za su rage ko kuma magance matsalar ta cin hanci, amma lamarin sai kara ta’azzara ya ke yi a nahiyar a cewar rahoton.

Sannan mafi yawan wadanda aka gudanar da binciken akansu, wadanda suka fito daga kasashe 18, sun ce basu gamsu da yadda gwamnatocinsu ke yaki da matsalar cin hanci da rashawa ba, musamman a fannin ma’aikatun gwamnati da suka hada da kotuna da na ‘yan sanda.

Sai dai duk da wannan sakamakon da binciken ya nuna, kungiyar ta Transparency ta ce akwai alamun nasara a yaki da wannan matsala a kasashen Botswana da Burkina Faso da Lesotho da kuma Senegal.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG