Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan awaren Kamaru Sun Yi Awon Gaba Da 'Yan Takarar Majalisa 40


Shugaba Biya na Kamaru
Shugaba Biya na Kamaru

Mayakan ‘yan aware na yammacin kasar Kamaru sun sace akalla ‘yan takara 40 da suke takarar majalisa da kananan hukumomi, a wani yunkuri na kawo cikas a zaben da aka tsara za’a gudanar a watan Fabrairu mai zuwa.

Gwamnati ta yi alkawarin kubuto da wadanda ake garkuwa da su da kuma kare ‘yan takara da jami’an zaben. Yayin da suke cewa tilas a gudanar da zabe mai inganci.

Dan shekaru 51 da haihuwa kuma malamin makaranta Wilson Bate ya ce ‘yan awaren dole su sako ‘yan kasar Kamarun da basu ci ba, basu sha ba, wadanda suke so su gudanar da abinda ya kamata da kundin tsarin mulki ya tanada musu.

Yace wannan abin kunya ne. Kuma banji dadin cewa ana garkuwa da ‘yan siyasa ba kawai saboda suna so su aiwatar da hakkinsu a matsayinsu na 'yan kasa. Gwamnati ya kamata ta yi dukan abinda ya kamata ta tabbatar cewa akwai wurare da za’a aiwatar da tarukan siyasa, kana su tabbatar sun samar da cikakken tsaro a wannan zaben mai zuwa.

'Yan awaren suna ta gwabza fada tun a shekarar 2017 don su raba Arewa maso yamma da kuma kudu maso yammacin Kamaru da suke magana da turancin Ingilishi daga sauran kasar da bangaren da suke da rinjaye da suke magana da Faransanci.

Sace-sacen suna zuwa ne a lokacin da ‘yan majalisar Kamaru suke wani taro don yin muhawara kan ba bada wani matsayi na musamman da shugaba Paul Biya ya bada umarni a yi da nufin warware rikicin ‘yan awaren.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG