Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindga A Zamfara Sun Rage Kudin Fansar Mutane 85 Da Ake Garkuwa Da Su


Buhari, hagu da gwamna Matawalle, dama (Hoto: Instagram)
Buhari, hagu da gwamna Matawalle, dama (Hoto: Instagram)

A karshe ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da mutane 85 a kauyen Wanzamai da ke cikin karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara sun amince su karbi Naira 20,000 kan duk wadanda aka sacen.

Sun kuma bukaci hukumomi da su janye sojoji daga kauyen a matsayin wani bangare na sharudan sakin wadanda aka sace.

Sun ba da karfe 12 na daren Lahadi a matsayin wa'adin, inda suka yi barazanar kashe duk wanda ya kasa biyan kudin a kan lokaci ko kafin lokacin da aka kayyade.

Jaridar Punch ta ci gaba da cewa 'yan bindidar sun yi barazanar cewa muddin ba a janye sojojin da aka tura kauyen Wanzamai ba za su ci gaba da yin garkuwa da mutanen kauyen.

Wani dan asalin yankin, Abubakar Na’Allah ya shaidawa jaridar Punch da ta rawaito labarin cewa, a wata tattaunawa ta wayar tarho ‘yan bindigar sun aike da sakon cewa za su karbi Naira 20,000 kacal daga kowane mutum a cikin mutane 85 da aka garkuwa da su a matsayin kudin fansa, la’akari da matsalar rashin kudi da suke ciki.

Na’Allah ya ce, “Tun da farko ‘yan fashin sun bukaci a biya su Naira miliyan 50 domin su sako mutane 85 da suka yi garkuwa da su wadanda galibinsu mata ne da kananan yara da suka je dajin neman itace ranar Juma’ar da ta gabata.

“Amma bayan jerin tattaunawar da aka yi, sun amince za su karbi Naira 20,000 daga kowane daya cikin mutanen saboda sun fahimci cewa dukkansu daga iyalai marasa galihu ne.

-Punch

XS
SM
MD
LG