WASHINGTON D.C. —
Akalla mutum 26 aka kashe ciki har da fararen hula bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a sasanin dakarun RSF, da ke wajen garin Kadugli da ke kudancin jihar Kordofan a Sudan ta Kudu
Tuni dai shugaban dakarun na RSF, Janar Hamdan Dagalo ya yi Allah wadai da wannan hari wanda aka kai shi a wannan mako.
Hukumomin garin na Kadugli sun ce maharan sun kaikaici sansanin dakarun ne sanye da kayan sarki.
Rahotanni sun ce baya ga wadanda suka mutu, wasu mutum 19 sun jikkata wadanda aka kwashe su zuwa Khartoum domin a yi musu magani, a cewar majiyoyin soji.
Bayanai sun nuna cewa, babu wanda aka kama sannan har yanzu ba a gane su waye maharan ba.
Facebook Forum