Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 18 A Kauyuka Biyu A Borno


Gidajen da 'yan Boko Haram suka kona a garin Benisheikh na Jihar Borno a watan Satumbar 2013
Gidajen da 'yan Boko Haram suka kona a garin Benisheikh na Jihar Borno a watan Satumbar 2013

Mutanen kauyukan Njaba da Kaya a Jihar Borno sun ce haka kwatsam suka ji karar harbe-harbe, sai kowa ya ranta cikin na kare.

Wasu ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ‘ya’yan kungiyar nan ce ta Boko Haram, sun hallaka mutane 18, suka kona gidaje masu yawa a hare-hare kan wasu kauyuka biyu a jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Wannan yana faruwa duk da matakan sojan da ake dauka na kare fararen hula a kauyukan dake karkara, wadanda kuma suka fi fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a yanzu.

Wani mazaunin kauyen Njaba, Wovi Pogu, wanda ya samu raunin harbin bindiga daga harin da aka kai aka kashe mutane 10 a kauyensu, yace “haka kwatsam muka ji karar harbe-harbe tare da kururuwar mata da yara kanana dake neman taimako.”

Pogu, wanda yake kwance a asibiti a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, ya ci gaba da cewa, “A lokacin da naje shiga gida na, an harbe ni a kafa, amma sai nayi ta ja har na shiga cikin wata bukka, inda na buya har na daina jin karar harbe-harben.”

A ranar laraba, ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne, sun harbe suka kashe mutane 8 a kauyen Kaya, sannan suka cinna wuta suka kona kauyen.

Mayakan Boko Haram, sun kashe dubban mutane a yankin arewacin Najeriya, inda Musulmi suke da rinjaye, a kyamfe din da suke ikirarin cewa na kafa dokokin Islama ne.

A wannan rana, shaidu sun ce mayakan sun kona wasu kauyuka guda biyu.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya a yankin arewa maso gabas, Kanar Mohammed Dole, yace bay a da Karin bayani a game da wadannan hare-haren.

Kungiyar Boko Haram it ace ke janyo barazanar tsaro mafi muni ga Najeriya, kasar da ta fi kowacce arzikin man fetur a nahiyar Afirka.
XS
SM
MD
LG