Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan bindiga Sun Hallaka Mutum 8 A Jihar Nejan Najeriya


Wani yanki da Boko Haram suka kai hari a Maiduguri (Mun yi amfani da wannan hoto ne don nuna misalin kone-kone
Wani yanki da Boko Haram suka kai hari a Maiduguri (Mun yi amfani da wannan hoto ne don nuna misalin kone-kone

Hukumomin jiha ta Neja sun tabbatar da aukuwar wadannan hare-hare.

Akalla Mutum 8 ne aka kashe a wasu hare-hare mabanbanta da wasu 'yan fashin daji suka kai a jihar Nejan Najeriya.

Bayanai dai sun nuna cewa maharan sun abka garin Ukuru dake yankin Karamar Hukumar Mariga inda suka hallaka mutane uku tare da kona Illahirin garin da wuta da kuma yin garkuwa da kimanin mutum 50 kamar yadda Hasan Sa'idu Bobi ya yi fadawa wakilin Muryar Amurka ta wayar salula.

“Sun mamayi jama’a duk da cewa an kashe su ba kadan ba amma sun mana ta’adi na kone –kone na gidaje da motoci na mashina, shaguna ba’a magana, sun kuma kwashe mutane sama da 50 maza da mata.”

A can garin Manigi ma dake yankin karamar Hukumar Mashegu, maharan sun kashe MutUM 5 tare da yin garkuwa da wasu da dama in ji wani da ya bukaci a sakaya sunansa.

Babu wani karin bayani daga Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Nejan, amma Gwamnatin Jihar ta tabbatar da kai hare haren.

Sai dai babu tabbaci akan yawan mutanen da aka kashe in ji Sakataren gwamnatin Nejan Ahmed Ibrahim Matane.

Wannan dai duk yana zuwa ne bayan sanarwar Gwamnatin Najeriya na cewa sojojin kasar za su Afkawa ‘yan fashin dajin da suka addabi jihar Neja.

TASKAR VOA: Fim Da Aka Shirya Kan Leah Sharibu Ya Samu Lambar Yabo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Kalubalen Da Masu Fama Da Lalurar Galhanga Ke Fuskanta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Tasirin Cibiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Yara Ta HopeXchange A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hukumomi Sun Fara Shirin Bada Gudumawar Jini A Fadin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG