Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahara Sun Hallaka Akalla Mutane 16 A Masallaci A Jihar Neja


‘Yan bindiga.
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:15 0:00

‘Yan bindiga.

Wasu mahara dauke da manyan bindigogi sun hallaka akalla mutane 16 a dai dai lokacin da suke cikin masallaci suna gudanar da sallar asubahin ranar Laraban nan a jihar Neja dake arewacin Nigeria.

Bayanai dai sun nuna yan bindigar sun abka wa masu sallar ne a kauyen garin Ba’are da ke yankin karamar Hukumar Mashegu, inda suka bude masu wuta a dai wannan lokaci kamar yadda wasu da suka tsallake rijiya da baya suka yi bayani.

Kawo lokacin hada wannan rahoto dai Muryar Amurka bata samu wani karin haske ba daga Gwamnatin jihar Nejan ba akan wannan al’amari,

To amma rundunar yan sandan Jihar Nejan ta tabbatar da kai wannan hari, sai dai ta ce Mutane 9 ne suka tabbatar da mutuwarsu,

Kwamishinan yan sandan jihar Nejan Monday Bala Kuryas yace sun kara tura karin jami'an tsaro a yankin.

Wannan dai shi ne karo na biyu da 'yan bindigar suka kai irin wannan hari ga masu sallah a jihar Nejan domin kuwa ko a kwanakin baya maharan sun kashe mutane 18 a dai dai lokacin da suke sallar asuba a garin Mazakuka dake yankin Mashegun.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Batsari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00


XS
SM
MD
LG