Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 26 A Wani Kwantan Bauna A Jihar Naija


Yan Bindiga
Yan Bindiga

Bayanai na nuni da cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi wa jami’an tsaron Najeriya kwanton bauna a yankin Zangeri da ke kan iyakar kananan Hukumomin Rafi da Wushishi, a daidai lokacin da jami'an sojojin ke kokarin hana ‘yan bindigar wucewa da daruruwan shanun jama’a da suka koro.

A hirar shi da Muryar Amurka, wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunan shi, yace cikin dare wayewar safiyar Litanin ne ‘yan bindigar su ka kashe sojojin suka kuma jikkata wadansu. Bisa ga cewarsa, an kashe sojojin ne a lokuta biyu duka a yanayin kwanton bauna.

A na shi bayanin, Sani Adamu, daya daga cikin jami’an tsaron sa kai da suka fafata da ‘yan bindigar a kauyen Kundu da ke daf da garin Zangeru, ya yi karin haske kan fafatawar da ya ce shi kanshi an harbe shi da bindiga ya kuma sami karaya a hannu. Bisa ga cewar shi, jami’an tsaron na sa kai, sun yi ido hudu da ‘yan bindigar lokacin da su ke farautarsu da jami’an soji, kuma babu ko jami’in soji daya a cikin tawagar tasu da ya dawo.

Sojojin Najeriya (Facebook/Rundunar sojin Najeriya)
Sojojin Najeriya (Facebook/Rundunar sojin Najeriya)

Daya daga cikin wadanda su ka kai gawarwakin asibiti da Muryar Amurka ta yi hira da shi ya ce, babbar bukatar al’ummar yankin ita ce ganin hukuma ta tura masu jami’an tsaro.

Shi ma a nashi bayanin, dagacin Zangeru Alhaji Tanko Madaki ya bukaci hukumomi su kai agajin gaggawa a yankin. Bisa ga cewarsa, mayakan sun sami galaba kan jami’an tsaron ne kasancewa mayakan sun saba da yankin, su kuwa sojojin baki ne, banda haka kuma ana tafka ruwa a daren lokacin da mayakan suka yi wa sojojin kwantan baunan.

Daga cikin sojojin da suka rasa rayukansu a harin akwai mai mukamin Manjo da kuma mai mukamin kyaftin.

Helikwafta
Helikwafta

Ko bayan wannan harin, Rundunar Mayakan Sama ta Najeriya ta sanar da cewa, wani jirginta mai saukar ungulu samfarin MI-717 da ke aikin jigilar wadanda su ka jikata a fafatawar da dakarun kasar ke yi da ‘yan bindiga a jihar Neja, ya fado da misalin karfe daya na ranar jiya Litinin a kusa da kauyen Chukuba kamar yadda kakakin Rundunar Air Kwamanda Edward Gakwet ya sanar, sai dai bai bada tabbacin adadin wadanda ke cikin jirgin ba, ko kuma tabbatar da cewa, ‘yan bindiga ne suka kakkabo jirgin, sai dai ya bayyana cewa, ana gudanar da bincike.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:

Yan Bindiga Sun Hallaka Sojojin Najeriya 26 A Jihar Naija
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG