Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Bindiga Sun Kai Hari a Kan Barikin Soja Nijar


Rundunar Sojin Nijer

Da sanyi safiyar yau Asabar ne wasu yan bindiga suka kai harin ta’addanci a kan barikin sojan Ayoru dake yankin Tilaberi a Jamhuriyar Nijar.

Rahotannin sun cewar yan bindigar da ake zaton sun ketaro ne daga kasar Mali sun kashe jami’an Jandarma da dama a wannan harin ta’addanci kana suka arce.

Hukumomin tsaro a Jmahuriyar Nijer sun tura jirgin sama mai saukar ungulu zuwa yankin da aka kai harin don ganin an kama maharan, matakin da dan majalisar yankin Tilaberi Karimu Buraima ya nuna shakkunsa a kai.

Wannan harin ya sa majalisar dokokin kasar ta dakatar da mahawara da ta shirya yi a yau a kan matsalar makamashi da Nijer ke fama da ita. Kwamitin tsaro na majalisar ya kira wani taron gaggawa don tattaunawa a kan wannan batu.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG