Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Kwamishinan Kimiyya Da Fasaha Na Jihar Katsina, Dr. Rabe Nasir Bindawa


Dr. Rabe Nasir Bindawa

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sanusi Buba, ya tabbatar da rasuwar kwamishinan da daren jiya Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a gidan marigayin da ke gidajen estate din Fatima Shema kamar yadda wasu majiyoyi suka rawaito.

Wasu mahara da ba a tantance ko su waye ba sun hallaka kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Katsina, Dr. Rabe Nasir Bindawa.

Wasu majiyoyi daga unguwar gidajen Fatima Shema Estate, unguwar da marigayin yake zaune, sun ce maharan sun kashe shi ne ta hanyar caka masa wuka a cikin dakinsa, kana kuma suka kulle gawarsa tana a bandakinsa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sanusi Buba, ya tabbatar da rasuwar kwamishinan da daren jiya Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a gidan marigayin da ke gidajen estate din Fatima Shema kamar yadda wasu majiyoyi suka rawaito.

Ya ce “Wannan mummunan al’amarin ya faru ne da daren jiya (Laraba) da daddare. Mun kwashe gawar kuma an fara bincike."

Kwamishinan 'yan sandan ya kara da cewa an kama wani mutum da ake zargi da hannu a kisan, yayin da ake ci gaba da bincike

“Ba ma son mu ba da wani karin bayani game da halin da ake ciki game da kisan. An kama wanda ake zargi kuma an fara bincike. An kai gawar zuwa cibiyar lafiya ta tarayya dake Katsina.”

Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari da wasu manyan jami’an gwamnati sun ziyarci gidan marigayin.

Ana sa ran za a yi jana'izar gawar kwamishinan yau Juma'a da karfe 2:00 na rana.

XS
SM
MD
LG