Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 24 A Jihohin Katsina Da Kaduna


‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga

Mutane 24 suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren ‘yan bindiga a jihohin Katsina da Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun kai wani hari a kauyen Duba da ke cikin karamar hukumar mulkin Batsari ta jihar Katsina a daren Lahadi, inda suka kashe mutane 12, suka kuma raunata wasu da dama.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Katsina Isah Gambo, ya shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar da adadinsu ya kai 300 dauke da manyan bindigogi, sun kai farmakin ne da misalign karfe 9 na dare.

Ya ce “da isar su a kauyen na Duba, ‘yan bindigar sun soma harbi ba kakkautawa wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 12, inda daga baya kuma suka farfasa shagunan, suka kuma yi awon gaba da dabbobin jama’a.”

To sai dai ya ce rundunar tsaron hadin gwiwar sojoji da ‘yan sanda na nan suna bin hanyoyin shawo kan matsalar.

Karamar hukumar mulkin Batsari dai ta kasance babbar matattarar ‘yan bindiga a jihar Katsina da yankin Arewa maso yammacin najeriya, kasancewar ta yi iyaka kungurmin dajin nan na Rugu, da kuma kananan hukumomi 10 da ke fama da matsalolin hare-haren ‘yan ta da kayar baya.

A jihar Kaduna ma an kashe akalla mutane 12 a hare-haren ramuwar gaya tsakanin ‘yan bindiga da mazauna kauyen Mado da ke cikin karamar hukumar mulki ta Zangon Kataf.

To sai dai kwamishinan tsaro da lamurran cikin gida Samuel Aruwan, ya ce ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu a hare-haren.

Ya ce ya zuwa yanzu an sami gano gawarwaki 9 na mutanen da suka rasu, da kuma wani mutum da ya sami rauni.

XS
SM
MD
LG