Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda ‘Yan sandan Jihar Nasarawa Suka Kama Mai Safarar Makamai


'Yan sandan Najeriya (Facebook/NPF)
'Yan sandan Najeriya (Facebook/NPF)

Kama mutumin na zuwa ne, a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalar ‘yan fashin daji da ke garkuwa da mutane don neman kudin fansa, musamman a arewa maso yammacin kasar.

‘Yan sanda a jihar Nasarawa da ke arewacin tsakiyar Najeriya sun ce sun cafke wani mutum da madaukin harsashin bindiga kirar AK-47 guda 53 da kuma ruwan harsashi 260.

A ranar Asabar aka kama Likita Abubakar mai shekara 35 wanda hukumomin taro suka ce sun jima suna bibiyan al’amuransa kan zarginsa da hannu a ayyukan fashi da garkuwa da mutane a cewar jaridar Vanguard.

Jaridar ta ruwaito Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar ASP Rahman Nansel tana cewa, an kama mutumin ne bayan da aka sanar da su cewa an gan shi a yankin mahadar Alusha da ke karamar hukumar Akwanga.

Rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa an kuma samu Abubakar da kudi naira dubu 35,000 baya ga maudikin harsashan.

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba (Facebook/NPF)
Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba (Facebook/NPF)

Jaridar Punch ta ce wata tawagar ‘yan sanda da ke sintiri ne a yankin na Akwanga ta cafke mutumin yayin da yake kokarin safarar makaman. Ta kuma ce an an kama shi ne da kudi naira dubu 38.

Bayanai sun yi nuni da cewa za a mika mutumin zuwa sashen binciken manyan laifuka na CID da ke Lafia, babbar birnin jihar Nasarawa.

Kama mutumin na zuwa ne, a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalar ‘yan fashin daji da ke garkuwa da mutane don neman kudin fansa, musamman a arewa maso yammacin kasar.

Da farko, akasari matafiya ne kan fada tarkon ‘yan bindigar wadanda akan yi awon gaba da su zuwa cikin daji har sai an biya kudin fansa.

Daga baya kuma lamarin ya yi kamari ya koma ana bin makarantu, inda akan sace daruruwan dalibai a shiga da su cikin daji.

A halin yanzu akwai daliban makarantar Islamiyyan Tegina sama da 100 da ‘yan bindigar ke rike da su a daji, wadanda aka yi garkuwa da su tun a watan Mayu.

Baya ga haka akwai daliban makarantar Yauri na jihar Kebbi da su ma suke hannun ‘yan fashin dajin baya ga daidaikun mutane da aka sace daban-daban a sassan arewa maso yammacin Najeriyar.

XS
SM
MD
LG