Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 27 A Gamboru-Ngala


Kangon wani gini a garin Benisheikh a Jihar Borno, bayan da 'yan Boko Haram suka kai farmaki a kan garin, 19 Satumba, 2013.
Kangon wani gini a garin Benisheikh a Jihar Borno, bayan da 'yan Boko Haram suka kai farmaki a kan garin, 19 Satumba, 2013.

Shugaban karamar hukumar Gamboru yace a ranakun laraba da alhamis, 'yan bindiga sun far ma garin dake bakin iyaka da Kamaru, suka kashe mutane 27

'Yan bindigar da aka yi imanin 'ya;yan kungiyar na ce ta Boko Haram, sun kashe mutane 27 a wasu hare-hare guda biyu da suka kai cikin makon nan kan garin Gamboru dake Jihar Borno, a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

A ranar laraba da daddare, 'yan bindigar sun abka cikin garin na Gamboru dake bakin iyaka da Kamaru, suka kashe wasu mutanen garin su 6.

Shugaban karamar hukumar Gamboru, Alhaji Modu Gana Sheriff, ya fadawa 'yan jarida cewa, kashegari ranar alhamis da daddare, 'yan bindigar sun sake komowa, suka kashe mutane 21.

Wata majiyar soja a Jihar Borno, ta fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuter cewa da alamun an tsara wadannan hare-haren guda biyu sosai, sannan ta gaskata labarin cewa mutane 21 aka kashe fararen hula.

An tsinke layukan tarho a jihar Borno a wani yunkurin birkita ayyukan 'ya'yan Boko Haram, abinda ya sa akan dauki kwanaki da dama kafin labarin duk wani hari ya kai Maiduguri, babban birnin Jihar.
XS
SM
MD
LG