Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Hudu, Sun Kuma Yi Garkuwa Da Akalla 40 A Arewa Maso Yammacin Najeriya


Yan bindiga a jihar Sokoto
Yan bindiga a jihar Sokoto

Kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a Afirka na fama da matsalolin tsaro da sosai da suka hada da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa a yankin arewa maso yammacin kasar, lamarin da ya kai makura.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Yazid Abubakar ya tabbatar da aukuwar harin, ya kuma ce an tura sojoji zuwa gundumar Kasuwar Daji da ke garin inda lamarin ya faru.

Mazauna yankin da suka hada da wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, sun yi bayani wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho game da halin da suke ciki a wannan al’amari, wanda ya fara da harin da aka kai ofishin 'yan sandan yankin.

Yan bindiga
Yan bindiga

"Harbe harben bindiga da aka yi ta yi a nan da can sun tayar da ni da misalin karfe 0100 agogon GMT. Sun fara da jami’an tsaro kafin su ka shiga gidajenmu," in ji Hussaini Mohammed.

Hussaini wanda ya yi nasarar tserewa ya kara da cewa, "Sun kama mata da yara sama da 40, ciki har da wasu dattijai maza."

Hamisu Kasuwa Daji wanda shi ne shugaban kungiyar direbobin sufuri na garin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa maharan sun kama dansa da jikokinsa biyu.

Wani bangaren ofishin ‘yan sanda da aka kaiwa hari.
Wani bangaren ofishin ‘yan sanda da aka kaiwa hari.

“Gidan nawa yana kusa da ofishin ‘yan sanda ne, ‘yan bindigar sun fara kai farmaki ofishin ‘yan sandan, inda suka kwashe mintuna da dama har su ka kashe ‘yan sanda biyu da wasu fararen hula biyu.

“Daga nan suka wuce gidana, wanda a lokacin na riga na gudu, bayan na dawo gida daga baya na gane sun tafi da dana da jikoki na biyu,” inji shi.

Kungiyoyin ‘yan bindiga dauke da muggan makamai wadanda ‘yan yankin ke kira mafasan daji, sun yi barna a yankin Arewa maso yammacin Najeriya a cikin shekaru uku da suka gabata, inda suka yi garkuwa da dubban mutane, tare da kashe daruruwan mutane da kuma hana tafiye tafiye ta hanya ko yin noma a wasu yankunan.

Tabarbarewar tsaro dai na kara tsananin matsalar tsadar rayuwa sakamakon sauye-sauyen da shugaba Bola Tinubu ya yi wanda har yanzu bai bayyana yadda ya ke shirin tunkarar matsalolin da ke kara ta'azzara ba.

~ REUTERS

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG