Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan bindiga Sun Kashe Mutum Biyu a Tsakanin Najeriya Da Jamhuriyar Nijar


Wani yanki da 'yan bendiga suka kai hari a Najeriya

Wadansu mutane da suka kai 50, dauke da manyan bindigogi ne, in ji mutanen garin Kwandamo a cikin karamar hukumar mulkin Illela ta Jihar Sokoto, da ke kan iyaka da birni N'Konni a Jamhuriyar Nijar suka kai harin.

Maharan sun afka garin, inda suka share kusan awa biyu suna sauke ruwan harsasai a cikin garin, suka kuma firgita jama'ar kafin su afkawa wani mutum bawan da suka sassare da adda bayan sun yi ta harbin sa ba tare da samun nasara ba.

Daya daga cikin mutanen garin ya ce, yana da kyau hukumomi su atallafa masu kasancewa a kowane dare, a wannan karamar hukumar mulkin ta Illela sai an dauke wani ko wata ko an kaiwa wani gari hari ko an kashe wani ko wata ko an yi garkuwa da mutane, wadanda sai an biga kudin fansa ake karbo su.

Jim kadan bayan ya dawo daga wurin ta'aziyar mutane biyu da a ka kashe a garin Kwandamo, shi ma suka kashe shi tunda, maharan sun hadu ne da daya daga cikin ‘yan bangan garin bayan sun kashe wannan magidancin da suka sassare, a cewar shugaban karamar hukumar mulkin Illela Injiniya Aliyu Salihu.

Su dai maharan, sai da suka dauki wani bawan Allah daga Gari Mai Ruwa kamin su afkawa garin Kwandamo, kuma bayan kwana guda da ya gabata wadansu maharan sun kai hari a Sonani inda suka dauke wani mutum guda.

Saurari rahoto cikin sauti daga Harouna Mamane Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:52 0:00


Matsalar Tsaro A Zamfara

Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Kamu A Auren Nupawa

Yadda Nupawa Suke Kamun Ango A Bikin Aure
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG