Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 19 A Wani Hari Da Suka Kai Wa Ayarin Motocin Mataimakin Gwamnan Kebbi


Yayin da ake jana'izar wasu mutane da 'yan bindiga suka kashe a arewacin Najeriya
Yayin da ake jana'izar wasu mutane da 'yan bindiga suka kashe a arewacin Najeriya

Akalla sojoji 19 ne aka kashe a jihar Kebbi, yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan ayarin motocin mataimakin gwamnan, kamar yadda mazauna garin suka bayyana a ranar Laraba.

An kai harin ne a ranar Talatar da ta gabata, yayin da kuma wasu ‘yan bindiga suka yi wa ‘yan kungiyar sa-kai ‘yan banga 62 kwanton bauna a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Mataimakin gwamnan jihar Sama'ila Dabai Yombe ya tabbatar da harin kwanton bauna na ranar Talata, ya kuma ce an yi artabu da bindiga a garin Kanya wanda ya yi sanadin asarar rayuka amma bai bayar da cikakken bayani kan adadin mutanen da aka kashe ba.

"Mun shiga cikin wani harin kwantan bauna da 'yan ta'adda suka bude wuta ga tawagar mu a lokacin da muka sha wani kwana a kan hanyarmu zuwa Wasagu," in ji Yombe.

An kai harin ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Talata, mazauna yankin sun ce an kashe sojoji 18 da dan sanda 1 yayin da wasu 8 suka jikkata.

“Na kirga gawarwaki 19 daga harin kwantan bauna da aka yi a ranar Talata a Kanya, an kuma loda su a cikin motocin daukar marasa lafiya guda biyu domin jigilar su zuwa Birnin Kebbi.” Inji Bashir Bala, wani dan jarida.

‘Yan bindiga sun baza tsoro a yankin arewa maso yamma, inda suke garkuwa da daruruwan yara ‘yan makaranta da mazauna kauyuka domin neman kudin fansa.

A watan Janairu, wasu ‘yan bindiga da dama a kan babura sun kai farmaki wani kauye tare da kashe mutane sama da 50 a Kebbi.

Rikicin dai ya kara ta’azzara matsalolin da ake fama da su a jihohin Arewacin Najeriya.

~REUTERS

XS
SM
MD
LG