A Jamhuriyar Nijar ‘yan bindiga sun hallaka wani hakimi Ali Mainassara a yankin Tilabery bayan da su ka sace shi a gidansa da ke kauyen Boni, kafin su ka cinna wa gidan wuta sannan su ka kwashe dukiyoyinsa.
A ranar Litinin din da ta gabata ne wasu mutanen da ke kiran kansu Mayakan jahadi suka kai samame a gidan Hakimin. Bayan sun kashe shi, su ka yi gaba da gawarsa, sai bayan kwana daya da faruwar al’amarin aka tsinci gawar shi.
‘Yan bindigar sun yi alkawarin sake komawa kauyen na Boni domin karbar haraji a hannun talakawa, lamarin da ya haifar da zaman zullumi a garin.
Rahotanni na cewa har zuwa yanzu dangin mamacin ba su dauki gawar dan uwan nasu ba, saboda gudun fuskantar fushin wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
A saurari rahoto daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 27, 2023
An Samu Take Hakkin Dan Adam Da Dama a Jamhuriyar Nijar - Rahoto
-
Janairu 25, 2023
Ma’aikatan Kasar Nijar Sun Fara Yajin Aiki Na Wuni Biyu
Facebook Forum