Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Sace Manoma 22 A Abuja


Ministan Abuja Mohammed Musa Bello
Ministan Abuja Mohammed Musa Bello

‘Yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Abaji inda suka yi awon gaba da manoma 22 a kauyen Rafin Daji da ke kan iyakar babban birnin tarayya Abuja da jihar Neja mai fama da matsalar tsaro.

ABUJA, NIGERIA - Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya shaida wa Muryar Amurka cewa manoman dai suna aiki ne a gonakinsu dabam daban, kwatsam sai ‘yan bindiga suka farmasu suka tattarasu zuwa daji.

‘Yan bindigar da suka kai farmakin dauke da manyan bindigogi sun yi ta harbi a sama ba kakkautawa kafin suka tafi da manoman, bayan haka suka kona wasu motocin aikin gona guda biyu.

Rundunar ‘yan sandan birnin Abuja ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta kuma ce jami'anta da ke yaki da ‘yan ta'adda da kuma wasu zaratan jami'ai daga rundunar aiki da cikawa, tuni suka fantsama cikin dajin don ceto mutanen da aka sace.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ASP Oduniyi Omotayo, wanda ya kara tabbatar da sace manoman a gonakinsu, ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba sai sun ceto manoman tare da kama maharan don su fuskanci hukunci.

Birnin Abuja dai na fama da matsalar ‘yan bindiga dadi kasancewar duk jihohin da ke makwabtaka da ita na fuskantar matsalar tsaro, musamman satar mutane dan neman kudin fansa.

A baya dai rundunar ‘yan sandan birnin tare da hadin gwiwar sauran jami'an tsaro da ma ‘yan sa kai sun sha kai samame a tsaunuka da dazuzzukan da ke kewaye da birnin Abuja inda ‘yan ta'addar ke kafa sansanoninsu.

Sai dai da alama ‘yan bindigar yanzu na daukar sabon salo musamman wajen ganin sun kauce fada wa hannun jami'an tsaro da suka tada kaimi wajen yaki da su da magance sauran matsalolin tsaro.

XS
SM
MD
LG