Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya Kusan 70 A Hanyar Kaduna Zuwa Birnin Gwari


Yan bindiga
Yan bindiga

Rahotanni sun yi nuni da cewa matafiya kusan 70 ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a ranar Laraba.

Lamarin ya faru ne a kusa da kauyen Udawa bayan Buruku a karamar hukumar Chikun ta jihar ta Kaduna kamar yadda wakilinmu a jihar ya shaida mana.

Rahotanni sun ce ‘yan bindiga da dama ne suka kai harin kan motocin da ke jigilar matafiyan, galibinsu ‘yan kasuwa ne, da safe inda daga bisani maharan suka tafi da su cikin dajin.

Saidai rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce ta sami nasarar ceto mutane 48 daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su din.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna Mohammed Jalige, ya ce jami’an ofishin ‘yan sanda na Buruku da ke raka fasinjoji a kan titin sun fuskanci harin da wasu ‘yan bindiga da ba'a tantance adadinsu ba da suka bude wuta kan motocin fasinjojin da ke tafiya.

Jalige ya kara da cewa, jami’an ‘yan sandan sun yi nasarar dakile harin ta hanyar amfani da karfin wuta kafin suka sami nasarar ceto matafiya 48 daga cikin fasinjojin.

A cewarsa, ba’a yi asarar rayuka daga bangaren jami’an ‘yan sanda da maharan ba, inda ya ce wadanda aka ceton na cikin koshin lafiya kuma daga baya suka ci gaba da tafiya.

Ko a ranar talata ma sai da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan hanyar ta Birnin Gwari, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu kana suka yi awon gaba da wasu mutane da ke cikin wata motar safa da ba’a iya tantance iya adadinsu ba, kamar yadda wani dan uwan daya daga cikin mutane biyu da suka rasa yan uwansu ya shaidawa wakilin mu a jihar ta Kaduna.

XS
SM
MD
LG