Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Sace Mutum 50, Sun Kuma Kona Gidaje A Jihar Zanfara


Kone konen gidaje a Jihar Zamfara
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:03 0:00

Kone konen gidaje a Jihar Zamfara.

‘Yan bindiga sun sace mutum 50 a wani hari da suka kai a unguwar Tungar Baushe a gundumar Mutunji, a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Bayanai sun tabbatar cewa an kona gidaje a wannan hari na daren jiya Laraba.

Tun da fari ‘yan bindigar sun bukaci mazauna Tungar Baushe su biya wani haraji da suka tsara domin kauce wa kai musu hari.

A maimakon haka, sai mazauna garin su ka zabi barin garin zuwa Ruwan Tofa, mai makwabtaka.

Matakin nasu, aka ce, ya fusatar da ‘yan bindigar, wadanda suka kai samame, kana suka nemi mutanen da suka baro unguwar ta Tungar Baushe.

Wani mazaunin unguwar ya ce “’Yan bindigar sun zo suka fara kone konen rumbun hatsi da gidajen mutane. Sun kamo wasu ‘yan unguwar da suka arce zuwa Ruwan Tofa domin neman matsuguni. Sun kuma je Tungar Baushe kana suka sace mutum 50.”

Ya ce “ Ba su yi sassauci ga kowa ba, har da mata da ma masu shayarwa. Daga nan ne suka shiga cikin jeji. Yanzu ne muke kirga asarar da aka yi bayan harin, koda yake babu wanda aka kashe a harin.”

Sai dai ya zuwa lokacin rubuta wannan labarin babu wata sanarwa a hukumance daga jami’an tsaro a kan wannan hari.

Wannan ne dai karon farko da aka kai babban hari tun bayan lokacin da gwamnatin tarayya ta ayyana Zamfara yankin da ba a tayar da jirgi.

A cewar mai Magana yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, gwamnati ta dau wannan matakin ne a kan wani zaton cewa wasu kananan jiragen ‘yan bindiga za su harba makamai.

Gwamnatin ta kuma haramta ayyukan masu hakar ma’adinai.

Karin bayani akan: Malam Garba Shehu, Zamfara, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG