Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Sace Wani Ma'aikaci A Afghanistan


Sojoin Afghanistan

Jami’an Afghanistan sun ce wadansu ‘yan tawaye da ba a gane ko su waye ba sun kashema’aikatan zubar da shararar mahakar ma’adanai tare da sace guda daga ma’aikatan.

Harin ya auku ne a safiyar yau litinin a lardin Kandahar dake kudancin kasar. Kakakin shugaban ‘yan sandan lardin yace ma’aikatan na gyara wurin ne domin a fara wani aikingirka bututun mai na biliyoyin daloli mai suna TAPI.

A farkon wannan shekarar dai kungiyar Taliban tayi alkawarin bada hadin kai domin cimma nasarar aikin, saboda yadda ta fahimci mahimmanci aikin ga kasar, kuma basu dauki alhakin kai harin ba.

An samo sunan TAPI ne daga kasashen da sukai hadin gwiwa domin yin aikin wato Turkmenistan, Afghanistan, Pakistan da India.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG