Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Yi Diran Mikiya Akan Madagali


Yawancin 'yan gudun jihiran daga jihohin Borno da Yobe suka fito yayin da wasu da dama sun fito ne daga wasu sassan Adamawa kamar daga kananan hukumomin Madagali da Michika, Yuni 3, 2014.

Hare- haren 'yan bindiga na karuwa a jihar Adamawa kamar yadda su keyi a Borno inda wasunsu sun yiwa Madagali diran mikiya jiya da asubahi.

Bisa ga alamu 'yan bindiga sun fara matsawa jihar Adamawa kamar yadda suka yiwa jihar Borno. Jiya da asubahi suka yiwa Madagali diran mikiya inda suka yi barna.

Mazauna garin na cewa da asubahin jiya 'yan bindiga suka dira garin na Madagali akan babura da motoci. Sun dira akan wani sansanin soja dake kusa da hanyar Gubula kana daga bisani suka kona sakatariyar gundumar raya kasa dake garin. 'Yanbindigan sun kashe soja guda da wani farar hula guda tare da raunata wasu. Sun kuma gudu da motocin sojoji guda biyu.

Saidai kuma jirgin yakin sojojin Najeriya da ya kawo dauki ya saka bam akan wata mijami'a wanda yayi sanadiyar mutuwar wata yarinya.

Shugaban karamar hukumar Madagali James Watarda ya bukaci a kawo masu daukin jami'an tsaro domin yanzu kullum ne 'yan bindiga ke kai masu hari.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG