Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindigar Da Ake Kyautata Zaton ‘Yan Boko Haram Ne Sun Kai Hari Kan Wani Kauye A Borno


wata mata zaune a gefen hanya da kayanta a bayan da 'yan bindigar Boko Haram suka kai farmaki kan garin Benisheik, September 19, 2013.

Hukumomi sun ce maharan sun kashe mutane 12, suka kona gidaje tare da satar motoci a wani gari mai suna Sandiya a Jihar Borno

Wasu ‘yan bindigar da ake kyautata zaton cewa ‘yan kungiyar nan ce ta Boko haram sun kashe mutane 12, suka kona gidaje da dama tare da satar motoci a yankin arewa masio gabashin Najeriya dake fama da ukubar yamutsi.

‘Yan sanda da mutanen garin Sandiya inda aka kai harin, sun ce wannan lamarin ya faru tun ranar alhamis, amma ba a fara jin labarin ba sai jiya asabar a saboda katsewar hanyoyin sadarwa na wannan yanki.

Jihar Borno tana daya daga cikin jihohi ukun da aka kafa dokar-ta-baci, kuma sojoji sun rufe hanyoyin sadarwa ta wayar salula baki daya a wani yunkurin hana tsagera tsare-tsaren kai hare-haren ta’addanci.

Kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Borno, Lawal Tanko, ya fada cikin wani sakon da ya aikewa da ‘yan jarida ta hanyar Email cewa “wasu bata-gari sun kai farmaki a kan garin (na Sandiya) suka kashe mutane 12.”

Yace sun kona gidaje da yawa, suka kuma sace ababen hawa a wannan gari mai tazarar kilomita 85 daga Maiduguri, babban birnin jihar.

Wani mazaunin garin na Sandiya, Sabitu Ali, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Faransa cewa ‘yan bindigar sun kai harin daukar fansa ne, a saboda su na zargin mutanen garin da laifin hada kai da jami’an tsaro wajen farauto ‘yan bindigar.

Malamin yace mahara su kimanin 30 sun shiga garin cikin kwmabar motoci su na kabbara su na harbi a kan kowa.

A cikin ‘yan watannin nan, ‘yan Boko Haram sun kai hare-hare a kan kauyu7ka da garuruwan dake cikin lungu kamar garin Sandiya, a yankin arewa maso gabashin kasar inda suka kashe daruruwan fararen hula.

Farmakin da sojoji suka kaddamar bayan kafa dokar-ta-baci a watan Mayu, ya samu nasarar korar ‘yan bindigar daga manyan garuruwa kamar Maiduguri, amma an ci gaba da kai hare-hare a kananan garuruwa da kauyuka da kuma kan hanyoyin mota.
XS
SM
MD
LG