Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindigar Da Suka Yi Garkuwa Da Hakimi A Jihar Kwara Sun Bukaci Kudin Fansa Naira Miliyan 60


'Yan Bindiga
'Yan Bindiga

Masu garkuwa da mutane da suka yi awon gaba da sakataren wata ma’aikata a jihar Kwara mai ritaya kuma hakimin garin Erubu na jihar, Dakta Zubair Erubu, sun kira iyalansa inda suka bukaci a biya su kudin fansa na naira miliyan 60.

Majiyoyi sun shaida cewa masu garkuwa da mutanen ba su ba da damar a tattauna da su ba, inda suka dage da cewa dole ne a biya kudin domin a sako shi, daga nan kuma su ka kashe layin watarsu nan take, kamar yadda gidan talabijan na Channels ya ruwaito.

Wani dan uwan hakimin da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa masu garkuwa da dan uwan nasu sun tuntubi iyalan ne da yammacin ranar Juma’a, yana mai cewa lamarin ya sanya su cikin rudani.

Erubu wanda kuma shine Magajin garin Erubu na masarautar Ilorin, ya kwashe kwanaki hudu a hannun masu garkuwa da mutanen, tun bayan da suka yi awon gaba da shi a ranar Alhamis din makon jiya.

Rahotanni sun yi nuni da cewa an far wa hakimin da kuma sace shi ne yana kan hanyar dawowa gidansa da ke yankin Ago-Oja na karamar hukumar Asa daga babban Ilorin, babban birnin jihar.

Haka kuma, rahotanni sun bayyana cewa Erubu ya kasance a garin Ilorin a ranar da lamarin ya faru inda ya je kula da wani majinyaci da ke kwance a asibitinsa mai zaman kansa da ke yankin Balogun Fulani a birnin Ilori.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ta Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya na mai cewa jami’an rundunar na bin diddigin masu garkuwa da Erubu, duk da cewa har yanzu ba su kai ga samun wani labari kan inda suka kai shi ba.

Ajayi ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin gudanar da aikin ceto domin ganin an sako Erubu daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi cikin lokaci.

XS
SM
MD
LG