Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari A Wani Masallaci a Arewacin Najeriya, Suka Kashe Mutane 16


Yan bindiga
Yan bindiga

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani kauye a arewacin Najeriya, inda suka kashe masu ibada akalla 16 a wani masallaci tare da yin garkuwa da wasu, in ji wani jami’in yankin.

Shugaban karamar hukumar Alhassan Isah Mazakuka ya ce an dauki tsawon sa’o’i ne a harin da aka kai kauyen Ba’are da ke yankin Mashegu a jihar Neja a ranar Alhamis din da ta gabata. Maharan da dama ne suka isa kan babura inda suka abka cikin kauyen, inda suka kashe mutanen da suke addu’a a masallacin, tare da kwasar ganima.

"Wadannan 'yan bindigar na da hatsari," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Associated Press a wata hira ta wayar tarho ranar Juma'a. "Sun kashe mutane 16 tare da yin garkuwa da dayawa daga cikin mutanenmu, ba ma san adadin da suka yi garkuwa da su ba saboda ba za a iya kirgawa ba."

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce mazauna yankin tara ne kawai aka kashe. A baya dai an zargi ‘yan sandan da raina alkaluman wadanda suka jikkata a irin wadannan hare-hare.

Harin dai shi ne na baya bayan nan a tashe-tashen hankulan da ke kara kamari a yankin arewa maso yammacin Najeriya da kuma arewa ta tsakiyar Najeriya inda kungiyoyin da ke dauke da makamai ke kai hare-hare kan al'umman yankunan, tare da kashewa da yin garkuwa da mutanen domin neman kudin fansa.

A farkon makon nan ne aka tabbatar da cewa an kashe matafiya 23 a wani yanki na daban na yankin arewacin kasar da ke fama da rikici.

Manyan gungun maharan dai galibi sun kunshi samari ne daga kabilar Fulani, wadanda a al'adance yawanci makiyaya ne da kuma rikicin da suka shafe shekaru da dama suna yi da al'ummar Hausawa manoma kan samun ruwa da filin kiwo.

Ga dukkan alamu ‘yan bindigar sun kara shiri da makamai, amma ba su fito fili suka bayyana wata manufa, ko dalili na siyasa ba. Ya zuwa yanzu kungiyoyin da ba su bin doka da oda - wadanda a kwanan baya wani gwamnan Najeriya ya ce sun haura 150 - ba su da suna ko kuma sanantattun shugabanni, amma a kwanakin baya kotu ta ayyana su a matsayin kungiyoyin ta'addanci.

Shugaban karamar hukumar Mazakuka ya ce, "Muna shan wahala da 'yan fashin (a nan)". “Abin da kawai muke bukata shi ne addu’a a yanzu, muna kukan neman goyon bayan gwamnati, gwamnati na iya bakin kokarinta amma har yanzu muna bukatar tallafi.

XS
SM
MD
LG